Rai Baƙon Duniya: Tsohon Alkalin Babbar Kotun Tarayya Ya Rasu a Borno

Rai Baƙon Duniya: Tsohon Alkalin Babbar Kotun Tarayya Ya Rasu a Borno

  • An shiga jimami bayan sanar da rasuwar tsohon alkalin Babbar Kotun Tarayya daga jihar Borno da ke Arewacin Najeriya
  • Mai shari'a Babagana Ashigar, ya rasu a Maiduguri bayan gajeruwar rashin lafiya, lamarin da ya jawo alhini tsakanin ma'aikatan shari'a da iyalansa
  • An yi jana'izarsa ranar Asabar bisa koyarwar addinin Musulunci, yayin da Babbar Kotun Tarayya ta bayyana cewa ya yi aiki da gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Babbar Kotun Tarayya ta mika ta'aziyya ga iyalan tsohon alkalinta da ya rasu tare da addu'ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa.

Tsohon alkalin Babbar Kotun, Mai shari'a Babagana Ashigar, ya rasu a garin Maiduguri da ke Borno bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Tsohon babban alkalin kotun tarayya ya rasu a Borno
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahotanni daga jaridar Tribune sun sun nuna cewa ya rasu a daren ranar Juma'a, 25 ga Yulin shekarar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda da babban jami'in rundunar sun mutu a Najeriya

Yaushe aka yi jana'izar marigayin a Maiduguri?

Bayan rasuwarsa, an gudanar da jana'izarsa ranar Asabar, 26 ga Yulin 2026, bisa tanade-tanaden addinin Musulunci.

Iyalan mamacin, abokai da sauran al'umma sun halarci jana'izar domin yi masa bankwana ta ƙarshe.

A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai ta Babbar Kotun Tarayya, Dakta Catherine Oby Christopher, ta fitar, kotun ta bayyana marigayin a matsayin fitaccen alkalin da ya yi aiki cikin ƙwazo da cikakken gaskiya.

Tsohon babban alkali ya rasu a Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum da marigayi Babagana Ashigar. Hoto: Professor Babagana Umaru Zulum, Aisha Baba Liman.
Source: Facebook

Gudunmawar da marigayin ya bayar kafin rasuwarsa

Sanarwar ta ce Mai shari'a Babagana Ashigar ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da adalci, inda ya gudanar da aikinsa cikin mutunci da rikon amana.

Ta ƙara da cewa gudummawar da ya bayar ga bangaren shari'a za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa, cewar Punch.

Kotun ta bayyana cewa abokan aikinsa, lauyoyi, ma'aikatan kotu da duk waɗanda suka yi hulɗa da shi sun amfana da kwarewarsa da kyawawan halayensa yayin da yake kan aiki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun magantu, sun tsuga miliyoyi na fansar alkalin babbar kotun Kebbi

Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayya, sauran alkalai, shugabanni da ma'aikatan kotun sun miƙa ta'aziyyarsu ga iyalan marigayin, ta yi addu'ar Allah Ya ba su ƙarfin zuciya da juriyar jure wannan babban rashi.

Haka kuma, sanarwar ta ƙara da addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

Rasuwar marigayin ya bar babbar gibi a Najeriya, inda za a ci gaba da tunawa da irin gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa gudanar da adalci a ƙasar.

Yan bindiga sun sace babban alkali a Kebbi

A wani labarin, an ji cewa yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza.

Hatsabiban 'yan bindigan sun yi awon gaba da shi daga gidansa da ke kan titin Zogirma a ƙaramar hukumar Bunza.

Rundunar ’yan sanda ta tura jami’an leƙen asiri da na musamman domin ceto alkalin wanda ya fada komar 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.