Saudiyya da Amurka Sun Hada Kai, Sun Farmaki Wasu da Ke Goyon Bayan Iran a Iraki

Saudiyya da Amurka Sun Hada Kai, Sun Farmaki Wasu da Ke Goyon Bayan Iran a Iraki

  • Amurka da Saudiyya sun kai hare-hare kan kungiyoyin da Iran ke marawa baya a Iraki bayan hare-haren jiragen sama marasa matuki
  • Saudiyya ta ce jiragen kariyarta sun kakkabo jirage marasa matuki, tana zargin mayakan da Iran ke goyon baya da kai hare-haren daga cikin Iraki
  • Kasashen biyu sun ce ba sa neman rikici, amma sun jaddada cewa za su kare kasashensu da kadarorinsu idan aka sake kai musu hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Amurka da Saudiyya sun kai hare-hare kan wasu wurare a gabashin Iraki bayan hare-haren jirage marasa matuki.

Majiyoyi suka ce kungiyoyin ne da Iran ke marawa baya ke amfani da su wajen shirya hare-haren jiragen sama marasa matuki kan cibiyoyin man fetur na Saudiyya.

Amurka da Saudiyya sun kai hari a Iraki
Shugaba Donald Trump da Dan Sarkin Saudiyya, Mohammed bin Salman. Hoto: Nathan Howard/Politico/Bloomberg.
Source: Getty Images

Saudiyya ta bayyana cewa tsarin kariyarta na sararin samaniya ya yi nasarar kakkabo wasu jirage marasa matuki da suka nufi cibiyoyin man fetur a yankin Gabashin kasar, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Iran: 'Ana kokarin goga mana kashin kaji kan harin Saudiyya'

Saudiyya ta zargi hare-hare daga Iraki

Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Saudiyya, Manjo Janar Turki Al-Malki, ya ce hare-haren ta'addancin sun fito ne daga cikin Iraki, inda kungiyoyin da Iran ke goyon baya suka kaddamar da su.

Ya ce Saudiyya na da cikakken hakkin kare kanta da kadarorinta, tare da mayar da martani a lokacin da ta ga ya dace bisa dokokin kasa da kasa.

Daga baya, Rundunar Tsakiyar Amurka (CENTCOM) da Ma'aikatar Tsaron Saudiyya suka sanar da kai hare-hare kan wasu sansanoni a gabashin Iraki da ake zargin ana amfani da su wajen jagorantar hare-haren jiragen marasa matuki.

Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta ce ba ta neman kara rura wutar rikici, amma za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko hari da za a sake kai mata, cewar rahoton DW.

Haka kuma, Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce hare-haren da kungiyoyin da Iran ke marawa baya suka kai sun zo ne a lokacin da masarautar ke kokarin rage tashin hankali a yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara fuskantar matsalar makamai, Trump ya dakatar da hare hare kan Iran

Sanarwar ta ce kungiyoyin sun karya dokokin kasa da kasa tare da yin watsi da ka'idojin kyakkyawar makwabtaka, duk da kokarin Saudiyya na samar da zaman lafiya a yankin.

Saudiyya da Amurka sun kai farmaki Iraki
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

Musabbabin Saudiyya na kai hare-hare

Saudiyya ta ce hare-haren da ta kai tare da hadin gwiwar CENTCOM sun kasance bisa tanadin Mataki na 51 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya ba kowace kasa damar kare kanta idan an kai mata hari.

Masarautar ta sake nanata cewa ba ta neman rikici, amma idan aka sake kai mata hari ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar duk matakan da suka dace domin kare 'yan kasarta da kadarorin kasa.

Rundunar CENTCOM ta kuma bayyana cewa an kakkabo dukkan makaman rokoki da Iran ta harba kan dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya, tana mai cewa rundunarta na ci gaba da kasancewa cikin cikakken shiri.

A karshe, Amurka ta gargadi cewa duk wani sabon hari kan dakarunta ko cibiyoyin makamashin Saudiyya na iya haifar da karin matakan soji daga bangarorin biyu.

Amurka ta ce Iran na rokon a yi sulhu

Kara karanta wannan

Najeriya ta jawo wa kanta, Amurka ta shirya dakile duk wani tallafi ga ƙasar

Mun ba ku labarin cewa sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana halin da ake ciki game da yakin Amurka da Iran da ake ci gaba da gwabzawa.

Rubio ya yi gargaɗin cewa Iran za ta ci gaba da fuskantar ƙarin matsin lamba idan ba ta sauya matsayinta a kan batun yarjejeniya ba.

Ya kuma yi ikirarin cewa ƙungiyar Houthi ta kasarYemen ta shiga matsala ne sakamakon tasirin Iran, tare da zargin cewa an yaudare ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.