Gwamnatin Abba Ta Dawo da Karfinta, Za a Kashe Biliyoyi Domin Ilmin Yaran Talakawa

Gwamnatin Abba Ta Dawo da Karfinta, Za a Kashe Biliyoyi Domin Ilmin Yaran Talakawa

  • Abba Kabir Yusuf zai kashe N8bn a gina sababbin makarantu uku masu dauke da kayan aiki na zamani
  • Gwamnatin jihar Kano ta kuma ware kudi domin gyara sauran makarantun firamaren da ake da su
  • Abba ya sanar da cewa an kashewa makarantun gaba da sakandare kudi domin a bunkasa ilmi a Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware N8bn domin gina katafaran makarantun firamare a fadin jihar Kano.

New Telegraph ta ce wadannan makarantu za su samu kayan aiki da duk abubuwan da ake bukata domin neman ilmi.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano zai inganta ilmi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Abba zai gina makarantun firamare a Kano

Za a gina makarantun ne domin yara masu basira da suka fito daga gidajen marasa karfi domin gobensu tayi kyau.

Kara karanta wannan

Kwanaki 5 da hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 sun ki taya Abba murnar galaba kan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a gina makarantun ne a kowace babbar mazaba da ake da ita a Kano.

...N6bn a kan gyaran sauran makarantu

Abba ya shirya kashe N6bn domin a gyara duk makarantun firamare da ke Kano.

Gwamna ya ce lokacin da dalibai za su rika daukar karatu a kasa a makarantun firamaren gwamnatin ya zo karshe.

Baya ga haka, Daily Trust ta ce gwamnatin NNPP ta amince a gyara cibiyoyin karatu 26 da Rabiu Kwankwaso ya gina.

Zuwa yanzu an gama gyaran 17 daga cikin wadannan makarantun koyon aiki da sana’o’i da ake zargin an yi watsi da su.

Kano: Abba ya koma kan jami'o'i

Mai girma Abba ya kuma batar da N500m domin a gina dakunan dalibai a jami’ar jiha ta Aliko Dangote da ke Wudil.

Kara karanta wannan

Bayan ya koma Kano, Gwamna Abba ya faɗi mutum 1 da ya cancanci yabo kan hukuncin kotun ƙoli

Abba ya yi ikirarin biyan N150m domin kirkiro sabon sashen ilmin yanayi a YUMSUK.

Gwamnatin NNPP mai-ci ta ce makarantar koyon ilmin shari’a ta Kano ta amfana da N100m domin fito da sababbin kwas.

Baya ga haka, gwamnatin ta ce ta biya 93% na kudin makarantar daliban da waje kuma an biya N1.5bn na kudin SSCE.

Ban da wannan, an kashe N700m a matsayin kudin karatun daliban Kano a BUK.

Sarakuna sun yi tsit bayan hukuncin kotu

A makon da ya gabata kotun koli ta ba Abba Kabir Yusuf gaskiya a shari'ar zaben gwamnan jihar Kano na 2023.

An ji labari masu martaba Aminu Ado Bayero, Nasiru Ado Bayero da sauran Sarakuna ba su taya NNPP murnar nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel