Kwamishinan ’Yan Sanda da Babban Jami’in Rundunar Sun Mutu a Najeriya
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da rasuwar manyan jami'anta guda biyu inda ta bayyana jimami kan babban rashin da aka yi
- AIG Adelek Olatunde ya rasu a gidansa da ke Legas bayan ritaya, yayin da CP Hassan Gwani ya rasu a wani asibiti da ke Egypt
- Rundunar ta ce jami'an biyu sun yi aiki da kwarewa, sadaukarwa da kishin kare rayuka, lamarin da ya jawo alhini da saƙonnin ta'aziyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta sanar da rasuwar manyan jami'anta biyu wadanda suka bayar da gudunmawa mai tsoka.
An ce tsohon Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan Sanda Adeleke Taiwo Olatunde da Kwamishinan 'Yan Sanda Hassan Saleh Gwani, sun rasu ciki kwanaki hudu.

Source: Twitter
Rundunar ta fitar da sanarwar ne ranar Talata, 28 ga Yulin 2026, ta shafinta na X, inda ta ce AIG Olatunde ya rasu a gidansa da ke Legas ranar 23 ga Yuli.
Manyan jami'an yan sanda 2 sun mutu
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda, CSP Ani Iniedu, ya bayyana cewa jami'an biyu sun yi fice wajen sadaukar da kai, aiki tukuru da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
An bayyana cewa Olatunde ya yi ritaya daga aiki a ranar 3 ga Nuwamban 2025, bayan ya shafe sama da shekaru 33 yana hidima cikin rundunar.
Ya shiga aikin 'yan sanda a ranar 18 ga Mayun 1992 a matsayin mataimakin sufetan yan sanda, sannan ya yi aiki a jihohi da sassa daban-daban na rundunar.
Daga cikin manyan mukaman da ya riƙe akwai DPO a Ikire, mataimakin kwamishinan yan sanda da na ayyuka a Western Port Authority Legas.
Haka kuma ya taba zama Kwamandan sashen SWAT na bangaren binciken manyan laifuffuka kafin daga bisani ya zama AIG bangaren ayyuka, mukamin da ya yi ritaya daga cikinsa.
Marigayin ya rasu ya bar matarsa da 'ya'yansa, yayin da abokan aiki da jama'a suka bayyana alhininsu tare da yi masa addu'o'i.

Source: Original
An yi rashin kwamishinan yan sanda
A gefe guda kuma, Kwamishinan 'Yan Sanda Hassan Saleh Gwani ya rasu ranar 19 ga Yulin 2026 yana karɓar magani a wani asibiti da ke Alkahira a ƙasar Masar.
Rundunar ta ce Gwani ma ya shafe kusan shekaru 30 yana hidima cikin kwarewa, gaskiya da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da walwalar al'umma.
Bayan sanarwar rasuwarsu, mutane da dama sun aika saƙonnin ta'aziyya, suna yabawa irin gudummawar da jami'an biyu suka bayar ga ƙasa da kuma addu'ar Allah Ya jikansu da rahama.
An haifi Gwani a shekarar 1970 a karamar hukumar Yamaltu Deba da ke jihar Gombe a Arewacin Najeriya.
Yan sanda sun nemi agajin IG a Najeriya
Kun ji cewa yan sandan MOPOL da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar Filato sun ce ba a biya su alawus na watanni bakwai ba.
Jami'an bayyana wadanda su ke zargi a cikin 'yan sanda da karkatar da kudin alawus da gwamnatin Filato ke fitarwa.
Sun roki Sufeto Janar na 'Yan Sanda da ya binciki lamarin tare da tabbatar da an biya su hakkokinsu duba da gudunmawar da suka bayar.
Asali: Legit.ng

