Rabin Amurkawa na Neman a Cafke Benjamin Netanyahu bayan Kai Ziyara a Kasar

Rabin Amurkawa na Neman a Cafke Benjamin Netanyahu bayan Kai Ziyara a Kasar

  • Wani sabon kuri'ar jin ra'ayi ta nuna kusan rabin Amurkawa na goyon bayan aiwatar da sammacin kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
  • Kashi 47 cikin 100 na mahalarta binciken sun ce suna ganin Netanyahu ya aikata laifukan yaki a Gaza, yayin da wasu suka zabi sabanin haka
  • Binciken ya zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan ikon gwamnatin Amurka wajen aiwatar da sammacin kama shi da Kotun ICC ta fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wani sabon binciken jin ra'ayi ya gudanar ya nuna cewa kusan rabin Amurkawa suna goyon bayan kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Majiyoyi suka ce hakan bai rasa nasaba da abin da ake zarginsa da aikatawa a yakin Gaza wanda ya jawo mabambantan ra'ayoyi.

Amurkawa da yawa na son kasarsu ta cafke Netanyahu yayin ziyararsa
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Donald Trump a fadar White House. Hoto: @netanyahu.
Source: Getty Images

Matsayar Amurka kan cafke Netanyahu

Kara karanta wannan

Amnesty na neman a cafke Netanyahu da ya je Amurka wajen Trump

Lokacin da aka tambayi mahalarta ko Amurka ta kamata ta aiwatar da sammacin kama da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta fitar kan Netanyahu, kashi 49 cikin 100 sun amsa da eh, cewar The Hill.

Sai dai kashi 27 cikin 100 sun ce a'a, yayin da kashi 23 cikin 100 suka bayyana cewa ba su da tabbacin matsayinsu kan batun.

Kotun ICC ta fitar da sammacin kama Netanyahu a watan Nuwamban 2024, tana zarginsa da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki da kuma aikata laifukan cin zarafin bil'adama.

Har ila yau, kotun ta zarge shi da kashe fararen hula da kuma kai hare-hare da gangan kan jama'ar Gaza, zarge-zargen da suka jawo cece-kuce a duniya.

A makon da ya gabata, magajin garin New York, Zohran Mamdani, ya janye daga alkawarin da ya taba yi na kama Netanyahu idan ya ziyarci birnin domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.

Mamdani ya ce gwamnatin birnin ba ta da ikon doka na aiwatar da sammacin, yana mai cewa gwamnatin tarayya ce kadai ke da wannan iko idan ta yanke shawara.

Ana ta maganar cafke Netanyahu a Amurka
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Zargin da ake yi wa Netanyahu

Kara karanta wannan

Yan sandan MOPOL sun nemi agajin Sufeton Ƴan sanda watanni 7 da hana su alawus

Duk da haka, Isra'ila da Amurka ba sa karkashin ikon hukuncin ICC, domin ba su amince da yarjejeniyar kafa kotun ba, ko da yake ICC na cewa tana da hurumi a yankunan Falasdinu.

Binciken ya kuma nuna cewa kashi 47 cikin 100 na mahalarta suna ganin Netanyahu ya aikata laifukan yaki a Gaza, yayin da kashi 24 cikin 100 suka ce bai aikata ba.

Sauran kashi 29 cikin 100 sun bayyana cewa ba su da cikakken tabbaci kan zarge-zargen da ake yi masa, cewar Truthout.

An gudanar da binciken tsakanin 25 da 27 ga Yulin 2026 tare da mahalarta 1,559, inda kuskuren sakamakon binciken ya kai kusan maki 3.3 cikin 100.

Shirin Amurka na nukiliyar Saudi ya firgita Isra'ila

An ji cewa yarjejeniyar nukiliyar da Amurka da Saudiyya suka cimma ta tayar da hankula a Isra'ila kan yiwuwar barkewar gasar mallakar makaman a yankin.

Tsofaffin shugabannin Isra'ila sun gargadi cewa shirin zai iya jefa yankin cikin sabon rikici tare da barazana ga tsaron ƙasar.

Yarjejeniyar za ta bai wa Saudiyya damar gina tashoshin makamashin nukiliya tare da tace sinadarin uranium domin shirin samar da makamashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.