Akwai Matsala: An Hango yadda Malaman Makaranta Masu Yawa Za Su Ajiye Aiki a Borno

Akwai Matsala: An Hango yadda Malaman Makaranta Masu Yawa Za Su Ajiye Aiki a Borno

  • Wani rahoto ya nuna cewa kusan 29% na malaman makarantu a yankunan da rikici ya shafa a Borno na fama da matsanancin damuwa, lamarin da ke barazana ga ci gaban ilimi
  • Binciken ya kuma bayyana cewa 65% na gidaje na da akalla yaro daya da ba ya zuwa makaranta, yayin da yawan 'yan mata masu barin karatu ya fi na maza
  • Masana sun bukaci gwamnati ta dauki karin malamai, ta kara horas da su kan kula da lafiyar kwakwalwa, tare da fadada shirye-shiryen koyarwa a yankunan da rikici ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja – Wani sabon rahoto da Cibiyar Nazarin Tattalin Arzikin Afirka (CSEA) ta fitar ya nuna cewa kusan 29% na malaman makarantu a yankunan da rikici ya shafa a jihar Borno na fama da matsanancin damuwa, lamarin da ke sanya da dama daga cikinsu tunanin barin aikin koyarwa.

Kara karanta wannan

Sakon da Tinubu ya aika Kaduna bayan umarnin a farauto 'yan bindiga

Rahoton, wanda aka fitar a Abuja ranar Talata, ya danganta wannan matsin lamba da matsalolin rashin tsaro, gudun hijira da kuma yawan katse harkokin ilimi a yankin Arewa maso Gabas.

Rahoto ya nuna cewa kashi 29 na malamai a Borno za su iya ajiye aiki.
Masu ruwa da tsaki yayin gabatar da rahoton binciken tashe tashen hankula da yadda suka shafi ilimi a Borno. Hoto: Solomon Odeniyi
Source: UGC

A cewar masu binciken, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya kara raunana tsarin ilimi a yankin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Rikici ya haddasa rufe makarantu

Binciken ya gudana ne a Maiduguri Metropolitan Council, Jere da Konduga, inda aka tattauna da gidaje 100, aka gudanar da bincike a makarantu 17, tare da tattaunawar kungiyoyi 80 da kuma hira da manyan masu ruwa da tsaki 57.

Rahoton ya nuna cewa kusan rabin makarantu sun taba rufewa sakamakon rikici da rashin tsaro, yayin da wasu kananan hukumomi suka samu raguwar yawan dalibai da kusan 37% tun daga shekarar 2020.

Har ila yau, an gano cewa 65% na gidaje na da akalla yaro daya da ba ya zuwa makaranta, yayin da yawan 'yan matan da ke barin karatu ya fi na maza da 23%.

Bukatar a karfafa malamai da tsarin ilimi

Rahoton Head Topics ya kuma bayyana cewa 62% na makarantu ba su da tsarin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar matsalolin rikici ko bala'o'i, abin da ke kara jefa makarantu cikin hadari.

Kara karanta wannan

'Yan kasa sun shiga tsaka mai wuya da gwamnati ta rufe YouTube, WhatsApp a Rasha

An bukaci jihar Borno ta kara zuba jari kan malamai
Taswirar jihar Borno inda ake fargabar malamai za su bar aiki. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sai dai binciken ya nuna cewa 52.9% na malamai sun samu horaswa cikin watanni 12 da suka gabata, yayin da 47.1% suka ce ba su samu isasshiyar horo ba.

Masu binciken sun ce ana bukatar daukar karin malamai zuwa yankunan da ke fama da rikici, kara ba su horo kan kula da lafiyar kwakwalwa, fadada shirye-shiryen koyarwa na gaggawa da na nesa, tare da inganta hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kungiyoyin farar hula domin farfado da ilimi a yankunan da rikici ya shafa.

An kore rahoton kai hari makarantar Borno

A wani labari, mun ruwaito cewa, ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi tir da yadda rahotanni suka rika cewa an kai hari Kwalejin 'Yan Mata ta Tarayya (FGGC) da ke Monguno a Borno.

Ma'aikatar ta bayyana cewa duk da akwai maganar an kai hari, amma lamarin bai shafi daliban da ke makarnatar tarayya ta 'yan matan da ake cewa ba.

Gwamnati ta tabbatar da cewa dukkan ɗalibai, malamai da kayan makarantar suna cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya ɓace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com