Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu mutane da suke kera bindigogi suna rabawa 'yan ta'adda a jihohin Arewa ta Yamma. An kama su da bindigogi biyar.
Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu mutane da suke kera bindigogi suna rabawa 'yan ta'adda a jihohin Arewa ta Yamma. An kama su da bindigogi biyar.
Fadar shugaban kasa ta zargi Adeniyi Adeyemi da kafa ma'aikatar bogi a Najeriya ba tare da sanin shugaban kasa Bola Tinubu da sauran hukumomin Najeriya ba.
Hukumar raya babban birnin Enugu (ECTDA), ta rufe ofisoshin kamfanin rarraba wutar lantarkin Enugu (EEDC) da ke a jihar Enugu kan datse wutar gidan gwamnati.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da sababbin hare-haren ta'addanci da 'yan bindiga suka kai a wasu kananan hukumomi biyu na jihar Katsina.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da 'yan Najeriya ta cikin jawabi a ranar dimukuradiyya. A gobe ne za a yi bikin ranar.
Wasu yan bindiga su hudu sun kai hari kan jami'an yan sanda a safiyar yau talata inda suka kashe yan sanda biyu da farar hula daya. Mutanen yankin suna zaman dar dar
Masu aikin ceto sun gano tarkacen jirgin da ya dauki mataimakin shugaban kasar Malawi,Saulos Chilima a dajin da ya yi hatsari a kasar, kuma an tabbatar da rasuwarsa.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa jihar ba ta amfana da komai ba, sakamakon zama karamin ministan tsaro da Bello Matawalle ya yi.
Majalisar dattijai ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na kara Naira biliyan 98.5 a kasafin kudin babban birnin tarayya na shekarar 2025.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya nuna adawarsa da kiran da ake yi na a samar da 'yan sandan jihohi a kasar nan. Gwamnan ya ce jami'an tsaron da ake da sun isa.
Rahotanni sun bayyana cewa wata gobara ta babbake ilahirin bangaren koyon ilimin fasaha da ke a cikin kwalejin fasaha ta Kano. Hukuma ta tabbatar da lamarin.
Labarai
Samu kari