Gwamna Dauda Ya Fadi Amfanin da Zamfara Ta Samu Silar Zaman Matawalle Ministan Tsaro

Gwamna Dauda Ya Fadi Amfanin da Zamfara Ta Samu Silar Zaman Matawalle Ministan Tsaro

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa jihar ba ta amfana da komai ba sakamakon zama ƙaramin ministan tsaro da Bello Matawalle ya yi
  • Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya samu muƙamin ƙaramin ministan tsaro a ƙarƙashin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Dauda Lawal ya bayyana cewa samun muƙamin da Matawalle ya yi, bai amfani jihar da komai ba a ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi magana kan amfanin da jihar ta samu sakamakon zaman Bello Matawalle ƙaramin ministan tsaro.

Gwamnan Zamfara ya bayyana cewa zaman tsohon gwamnan jihar ƙaramin ministan tsaro bai amfani jihar da komai ba.

Kara karanta wannan

"Yan bindiga sun shiga uku," Gwamna ya sha alwashin dawo da zaman lafiya duk runtsi

Dauda Lawal ya caccaki Bello Matawalle
Gwamna Dauda Lawal ya ce zaman Matawalle minista bai amfani Zamfara ba Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunrise Daily' a ranar Talata, 11 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Dauda yace kan zaman Matawalle minista?

Da yake amsa tambaya ko samun ministan ya amfani jihar Zamfara, gwamnan ya bayyana cewa zaman Matawalle ƙaramin ministan tsaro bai taimaka ba wajen ƙoƙarin magance matsalar tsaron da ta daɗe tana addabar jihar.

"Ana yawan yin magana kan batun ƙaramin ministan tsaro. Eh shi ne ƙaramin ministan tsaro, amma da me hakan ya amfane mu?"
"A ƴan makonni da suka wuce, ƴan bindiga sun je mahaifarsa, sun hallaka mutane da dama, me ya yi a kan hakan?"
"Eh muna da ministan tsaro amma wane amfani ya yiwa jihar Zamfara?"

- Dauda Lawal

Meyasa gwamna Dauda ya kafa rundunar tsaro?

Kara karanta wannan

Gwamna ya nuna adawa da kafa 'yan sandan jihohi, ya fadi dalilansa

Gwamnan ya koka kan halayyar da sojoji da ƴan sanda suke nunawa a ƙoƙarin shawo kan matsalar rashin tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a jihar.

Ya bayyana wannan halayyar ta hukumomin tsaron waɗanda suke ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya, ya sanya shi ya ƙirƙiro rundunar tsaron jihar wacce ake yiwa laƙabi da Askarawan Zamfara.

Matawalle ya raba raguna a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle ya raba raguna 4,860 ga al'ummar jihar.

Ƙaramin ministan ya kuma ware Naira miliyan 390 domin rabawa magoya bayan jam’iyyar APC da masu ƙaramin ƙarfi wanda hakan na daga cikin al’adarsa a lokacin irin waɗannan bukukuwan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng