Obasanjo Ya Yi Magana kan Sake Faruwar Yakin Basasa a Najeriya
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi gargadi cewa Najeriya ba za ta iya fuskantar wani yaƙin basasa na biyu ba bayan wanda aka yi a baya
- Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu ba a magance wasu daga cikin matsalolin da suka haifar da yaƙin basasa daga 1967 zuwa 1970 a Najeriya ba
- Haka zalika ya yabawa waɗanda suka tattara tarihin kisan gillar Asaba, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen hana sake faruwar irin haka a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi gargadin cewa Najeriya ba za ta iya sake fuskantar wani yaƙin basasa ba.
Ya yi magana yana mai cewa har yanzu da dama daga cikin abubuwan da suka haddasa yaƙin basasar 1967 zuwa 1970 suna nan ba a magance su ba.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a ɗakin karatu na OOPL da ke Abeokuta, jihar Ogun, lokacin da yake karɓar kundin tarihin kisan gillar Asaba daga hannun Isama Ajie na Asaba, Cif Chuck Nduka-Eze.
Littafin da aka wallafa kan Asaba
Littafin mai taken Asaba Massacre ya ƙunshi rubuce-rubuce da kuma shirin bidiyo da aka shirya bisa shaidun waɗanda suka ga abin da ya faru da idanunsu, tattaunawa da mutane, takardun tarihi, bidiyoyi da kuma binciken tarihi.
Da yake jawabi yayin karɓar aikin, Obasanjo, wanda ya kasance kwamandan soja a lokacin yaƙin basasar Najeriya, ya ce yana gujewa yin bayani kan kisan gillar Asaba saboda yankin yana ƙarƙashin jagorancin marigayi Janar Murtala Muhammed a lokacin.
Ya yaba wa Nduka-Eze bisa tattara tarihin abin da ya faru, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen adana tarihin Najeriya da kuma hana sake aukuwar irin wannan masifa.
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma tuna yadda a lokacin yaƙin ya hana wani soja yi wa wata mata fyade a Asaba, yana mai cewa irin wannan aiki yana da kyau.

Source: Facebook
Batun sabon yaki basasa
Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan halin da ƙasar ke ciki a yanzu, yana mai cewa har yanzu ba a magance da dama daga cikin matsalolin da suka haifar da yaƙin basasa ba.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
“Wasu daga cikin abubuwan da suka kai ga yaƙin basasa har yanzu suna nan. To, har yaushe za su ci gaba da kasancewa tare da mu?”
Da yake tuna wata magana da tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, ya taɓa yi, Obasanjo ya ce Najeriya ba za ta iya shiga wani yaƙin basasa ta fita lafiya ba.
Ya ce:
“Saboda haka, Allah Ya kiyaye mu da sake samun wani yaƙin basasa. Dole ne mu san abin da ya faru a baya, mu yi Allah wadai da abin da bai kamata ya faru ba, sannan mu yi duk abin da za mu iya domin tabbatar da cewa ba zai sake faruwa ba.

Kara karanta wannan
Abin da gwamnatin Katsina ta ce da aka kama shugabannin ƴan ta'adda a filin jirgi
Obasanjo ya je taro Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya je nadin sarauta fadar Sarki Muhammadu Sanusi II a Kano.
Sanata Rabiu Kwankwaso da dan takarar gwamna na NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo na daga cikin manyan NDC da suka taka wa Obasanjo baya.
Mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo da wasu manyan jami'an gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun hallara wajen nadin sarautar.
Asali: Legit.ng

