Canji Ya Tabbata, An Bayyana Sabon Kayan Aikin Bautar Kasa na NYSC a Najeriya

Canji Ya Tabbata, An Bayyana Sabon Kayan Aikin Bautar Kasa na NYSC a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da sabon kayan da masu yiwa kasa hidima (NYSC) za su rika amfani da su
  • Ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande ya tabbatar da cewa an maye gurbin khakin NYSC da tufafin kamfala (Adire)
  • Haka zalika ya ce za a fara tura masu yi wa kasa hidima wuraren aiki bisa fannin da suka karanta a makarantu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya tabbatar da cewa daya daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta amince da su a Hukumar Yi wa Kasa Hidima (NYSC) shi ne sauya khaki.

Ministan ya sanar da cewa daga yanzu, gwamnatin tarayya ta maye gurbin khakin NYSC da tufafin Adire watau kamfala da ake kerawa a gida Najeriya.

Kara karanta wannan

An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi

Ayodele Olawande.
Ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande yana magana a wurin taro Hoto: Ayodele Olawande
Source: Twitter

Olawande ya bayyana haka ne a shirin The Morning Brief na tashar Channels TV a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, 2026.

Ministan ya ce matakin na da nufin bunkasa masana'antu na cikin gida tare da tabbatar da cewa kudin gwamnati na ci gaba da zagayawa a tattalin arzikin Najeriya.

Ssbon khakin da aka sauya wa NYSC

Da aka tambaye shi ko za a rika kera sababbin kayan NYSC a cikin Najeriya, Olawande ya ce:

"Kamfala (Adire) za a koma amfani da ita. Ana kera ta a Najeriya, muna da shi a Ogun, muna da shi a Kwara, sannan muna da masana'antun yadi. Ya kamata mu rika mayar da kudinmu cikin kasarmu."

Yadda za a rika tura matasan NYSC aiki

Ministan ya kuma bayyana cewa a karkashin sabon tsarin da aka kawo wa NYSC, za a rika tura masu yi wa kasa hidima wuraren aiki bisa fannin da suka karanta.

Kara karanta wannan

Amupitan: Shugaban INEC ya dauko batun satar akwatin zabe da magudi gabanin 2027

Ya ce, misali, wadanda suka karanci ilimi za a tura su makarantu maimakon tsarin da ake amfani da shi yanzu, inda ake tura mutane ba tare da la'akari da kwarewarsu ba.

Olawande ya ce:

"Bayan kun kammala horo a sansani, ba za a tura ku makaranta kawai saboda NYSC ta ga dama ba, sai dai bisa tsarin da kuka bi tun kuna sansani. Wannan zai ba da damar sanin inda ya dace a tura kowane mutum."

Sojoji za su ci gaba da kasancewa a NYSC

Ministan ya musanta rahotannin da ke cewa za a cire rundunar soji daga harkokin. Yan bautar kasa watau NYSC, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Ya ce wannan fahimta ba daidai ba ce, yana mai bayyana cewa duk da cewa shugaban gudanarwar hukumar zai kasance farar hula, sojoji za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron masu yi wa kasa hidima.

NYSC.
Matasa masu yiwa kasa hidima suna fareti a sansanin horo na NYSC Hoto: @NYSC_NG
Source: Facebook

A cewarsa:

"Ba mu cire sojoji daga NYSC ba. Ba zai yiwu a cire su ba. Abin da ake nufi shi ne za a koma tsarin jagoranci na farar hula maimakon tsarin da ya fi karkata ga soja."

Kara karanta wannan

Kiristoci sun samu dama a shirin auren gata da Gwamna Abba zai ƙara yi a Kano

Dalilin Tinubu na sake fasalin NYSC

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta amince da gyare-gyaren da aka yi wa tsarin yi wa kasa hidima na NYSC.

Shugaba Tinubu ya ce gyare-gyaren na da nufin wadatar da matasan Najeriya da fasahohin zamani da kuma shirya su domin ci gaban kasa.

Haka kuma shugaban kasar ya bayyana cewa gyare-gyaren , wadanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da su, na daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262