Yadda Bukola Saraki Ya Kalubalanci Buhari kan Cin Bashi a Gwamnatinsa
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce ya bayyana takun-saka da aka yi da shi lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari
- Saraki ya ce ya kalubalanci gwamnatin a wancan lokaci kan buƙatun rancen ƙasashen waje da Majalisar Dattawa ta nace sai an tantance
- Tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya bukaci ƙarfafa gaskiya, ingantattun cibiyoyi, cinikayya, ilimi da kirkire-kirkire domin samun ci gaba mai ɗorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Como, Italy - Tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki ya tuna lokacin da yake Shugaban Majalisar Dattawa tsakanin 2015 da 2019.
Saraki ya ce a wancan lokaci sun dage wajen tabbatar da sa ido kan harkokin kuɗi da kasafin kuɗi.

Source: Twitter
Saraki ya bayyana haka ne a ranar Talata 30 ga watan Yunin 2026 yayin wani taro a Como da ke kasar Italiya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Masoyin Tinubu ya hango matsala, ya magantu kan tsawaita wa'adin shugaban Kwastam
Yadda Majalisar dattawa ke binciken kudi
Bukola Saraki ya ce majalisar ta gudanar da buɗaɗɗun zaman kasafi, ta binciki kuɗaɗen shiga da ba a tura baitul mali ba, tare da yunƙurin gyaran harkokin man fetur.
Saraki ya ce ya kalubalanci gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari kan buƙatun rancen ƙasashen waje, yana mai cewa dole ne a tantance manufa da tasirin kowane rance.
Ya ce:
"Na fuskanci hakan da kaina lokacin da nake Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, inda na kalubalanci bangaren zartarwa kan amincewa da rancen ƙasashen waje, kuma na gamu da gagarumin matsin lambar siyasa saboda tsarin bai kasance an gina shi domin bai wa cikakken bincike kan manufar rancen ko tasirinsa dama ba."
Ya bayyana cewa matsin lambar siyasa ya biyo bayan matakin majalisar na ƙin amincewa da rance ba tare da cikakken bincike ba.

Source: Facebook
Damuwar da Saraki ya nuna kan karancin kudi
A cewarsa, an karɓi yawancin rancen kamar kyauta ne, alhali kuwa akwai nauyin biyan su a gaba.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: An farmaki 'dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a wurin jana'iza
Saraki ya nuna damuwa kan ƙarancin kuɗaɗen haraji da Najeriya ke tattarawa idan aka kwatanta da girman tattalin arzikinta.
Ya ce rabon haraji da tattalin arzikin Najeriya kusan kashi shida cikin ɗari ne, wanda yake ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta a duniya.
Ya ce wannan sakamakon zaɓin siyasa ne, kuma shugabanci nagari zai iya sauya hakan, cewar rahoton Punch.
Saraki ya bukaci ƙasashen Afirka su rage dogaro da tallafin ƙasashen waje, su mayar da hankali kan kasuwanci, masana'antu da ƙara wa kayayyaki ƙima.
Ya ce rage tallafin ci gaba daga Amurka na iya zama dama ga Afirka ta sake fasalin dabarun ci gabanta.
Ya kuma bukaci ƙarfafa haɗin gwiwa da Turai, China, India, ƙasashen Gulf da sauran tattalin arzikin da ke tasowa bisa anfani na bai ɗaya.
Saraki ya wanke Tinubu kan gwamnatin Buhari
An ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya tuna baya kan abubuwan da suka faru da shi a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Bukola Saraki ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga zargin ya taka rawa wajen ganin an tuhume shi.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya nuna cewa Tinubu bai da irin wannan tasirin a wancan lokacin.
Asali: Legit.ng