Sanadin Mutuwa da Abubuwa 5 da ba a Sani ba kan Mataimakin Shugaban Kasar Malawi

Sanadin Mutuwa da Abubuwa 5 da ba a Sani ba kan Mataimakin Shugaban Kasar Malawi

  • An shiga alhini a kasar Malawi yayin da gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima a wani hatsarin jirgin sama
  • Marigayin mataimakin shugaban kasar ya mutu ne a hatsarin jirgin sama dauke da mutane 10 a hanyarsu ta dawowa gida inda nan ne yanayi ya rikice
  • Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera da ya tabbatar da mutuwar mataimakinsa tare da bayyana shi a matsayin jajirtattacen abokin aiki kuma uba na gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Malawi - Masu aikin ceto sun gano tarkacen jirgin da ya dauki mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Chilima a dajin da ya yi hatsari.

Kara karanta wannan

"An maida rai ba komai ba," Atiku ya riga shugaban kasa ta'aziyyar kisan Katsina

Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ya bayyana cewa an gano yadda hatsarin jirgin da ya yi sanadiyyar mutuwar mataimakinsa ya auku.

Saulos Chilima
Mataimakin shugaban kasar Malawi ya mutu a hatsarin jirgin sama Hoto: Saulos Klaus Chilima
Asali: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa jirgin ya daki wani dutse ne, sannan ya tarwatse da dukkanin fasinjojin da ke cikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu mutum ko daya da ya rayu a hatsarin jirgin dauke da mutane 10 har da mataimakin shugaban kasar.

Tarihin marigayi mataimakin shugaban kasar Malawi

1. Haihuwar Saulos Chilima

An haifi marigayin mataimakin shugaban kasar a ranar 12 Fabarairu 1973, wanda ke nufin ya mutu ya na da shekaru 51 a duniya.

An haife shi cikin iyalin Handerson a asibitin Queen Elizabeth da ke kasar Malawi. Kuma ya rayu cikin 'yan uwansa a kauyen Blantyre, inda ya ke yawan zuwa hutu wurin kakanninsa a Lilongwe da Ntcheu.

2. Karatun tsohon mataimakin shugaban Malawi

Mista Chilima ya yi karatunsa na Firamare a HHI Dharap, sakandare kuma a Marist Brothers Mtendere da ke Thiwi a gundumar Dedza.

Kara karanta wannan

Malawi: Jirgin mataimakin shugaban ƙasa ya yi hatsari, mutanen ciki sun mutu

Marigayin ya yi karatun digiri na biyu a bangaren ilmin kula da bayanai da digirin digirgir a kasar Birtaniya .Ya yi digiri a fannin kimiyyar dan Adam jami'ar Malawi.

3. Rayuwa da Iyali

Saulos Chilima ya rayu a tafarkin addinin kirista na darikar katolika, ya mutu ya bar matarsa daya Mary. Da yara biyu, Sean da Elizabeth. Ya rayu tare da iyayensa, Lilongwe da Elizabeth a kasar Malawi.

4. Siyasa

A watan Fabarairu 2014 Chilima ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasara karkashin jam'iyyar DPP tare da dan takara shugaban kasa Peter Mutharika.

Daga baya ya bar DPP zuwa UTM a shekarar watan Yuni 2018 domin tsayawa takara a 2019. Daga baya jam'iyyarsa ta shiga hadaka da ta bawa gwamnatin inda aka yi zaben da hadakarsu ta zo na uku.

Daga bisani aka soke zaben tare da sake yinsa a shekarar 2020 inda ya yi takara da a matsayin mataimakin Lazarus Chakwera.

Kara karanta wannan

Jirgin sama ya yi ɓatan dabo ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi da mutum 9

5. Zargin badakalar kwangila a Malawi

A shekarar 2022, an cire kariyar da yake da ita na gwamnati biyo bayan samunsa da shiga badakalar $150m na kwangilar gwamnati, a Nuwamba, 2022 kuma aka tuhume shi da karbar $280,000 daga hannun baamurke Zuneth Sattar domin ba kamfaninsa kwangila.

Saulos ya musanta zarge-zargen, daga bisani a shekarar 2024 gwamnati ta janye tuhumar da ake yi masa.

Shugaban Malawi, Saulos Chilima ya mutu

Aljazeera ta ruwaito cewa an gano tarkacen jirgin ne bayan kwana guda da batansa saboda mummunan yanayin da aka fuskanta a kasar.

Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ya shiga alhini bayan ya tabbatar da mutuwar mataimakinsa, Saulos Chilima mai shakearu 51 a hatsarn jirgin sama.

Jirgin ya dauke da mutane 10 ya bace a dajin Chikangawa, yayin da aka yi ta nemansa kafin daga baya a tarar da tarkacen da ya ragu bayan hatsarin, kamar yadda BBC ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki matakan inganta ilimi a Kano

Shugaban kasa Chakwera ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen dan kasa, kuma uba na gari ga iyalansa.

Ya yiwa 'yan kasar ta'aziyya, tare da bayyana cewa zai yi rashin abokin shawara na gari. Shugaban kasar Malawi da mataimakinsa dai ba jam'iyyarsu daya ba, amma sun yi hadakar siyasa a 2020 domin tafiya tare.

An rasa jirgin mataimakin shugaban kasar Malawi

A wani labarin kuma kun ji cewa jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban kasar Malari, Saulos Chilima ya yi batan dabo a hanyarsa na koma gida.

Mataimakin shugaban kasar na hanyarsa ta dawowa daga ta'aziyyar tsohon minista Ralph Kasambara ne aka samu sauyin yanayi, kuma aka nemi jirgin aka rasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.