Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Rikita Lissafin Jami'o'in Kano da Wasu Jihohi Arewa 2
- Kungiyar ASUU ta gargadi gwamnatocin Kano, Kaduna da Jigawa kan jinkirin aiwatar da yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a 2025
- Ta yi barazanar cewa ci gaba da kin aiwatar da yarjejeniyar na iya jawo sabon tsaiko a kalandar karatun jami'o'in waɗanna jihohi
- ASUU ta kuma nuna damuwa kan matsalar tsaro da kuma ƙin biyan wasu haƙƙokin malaman jami'o'i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ta gargadi gwamnatocin jihohin Kano, Kaduna da Jigawa kan rashin aiwatar da yarjejeniyar 2025.
Ta ce rashin aiwatar da wannan yarjejeniya da aka cimma tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU a jami'o'in Kano, Kaduna da Jigawa na iya haifar da tsaiko ga harkokin karatu.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce kungiyar ta bayyana cewa yayin da jami'o'in gwamnatin tarayya suka fara aiwatar da yarjejeniyar, babu ko daya daga cikin jami'o'in jihohin da ke karkashin shiyyar Kano da ta qbi sahu.

Kara karanta wannan
ASUU ta koka kan rashin cika alƙawari, ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami'o'i 11 a Najeriya
An kai ASUU bango a shiyyar Kano
Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano, Kodinetan shiyyar, Kwamared Abdulrazaq Ibrahim, ya ce hakurin ASUU ya kare bayan tsawon lokaci ana jinkirta aiwatar da yarjejeniyar.
Ya ce:
"Muna kira ga gwamnatocin Kano, Kaduna da Jigawa da su gaggauta aiwatar da dukkan tanade-tanaden yarjejeniyar da aka rattabawa hannu.
"Duk wani ci gaba da jinkiri ko aiwatar da wasu sassa kawai zai kawo cikas ga zaman lafiya tsakanin gwamnati da malaman jami'o'i tare da dagula kalandar karatu."
Abin da yarjejeniyar 2025 ta kunsa
ASUU ta bayyana cewa yarjejeniyar 2025, wadda aka cimma bayan shekara takwas ana tattaunawa, ta kunshi biyan bashin albashi na CATA, SAA da kuma alawus din EAA.
Kungiyar ta ce jihohin Bauchi, Ekiti, Osun, Benue da Sokoto sun riga sun fara aiwatar da yarjejeniyar, lamarin da ya kara fito da rashin bin ka'ida a jami'o'in shiyyar Kano.
Ta bukaci iyaye, dalibai, kungiyoyin farar hula da kafafen yada labarai su matsa wa gwamnatocin Kano, Kaduna da Jigawa lamba domin su aiwatar da yarjejeniyar, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC

Source: Facebook
ASUU ta ja kunnen jami'o'in shiyyar Kano
Kungiyar ta kuma gargadi ma'ajiyan kudin jami'o'i da su daina cire haraji daga kudaden alawus din CATA, tana mai cewa yarjejeniyar ta ware wannan alawus daga biyan haraji.
Haka kuma ta yi watsi da kin amincewar gwamnatin tarayya wajen biyan albashin watanni uku da rabi da aka rike wa malaman jami'o'i bayan yajin aikin da suka yi.
Shiyyar Kano ta ASUU ta hada da Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, da jami'ar Northwest (NWU) da ke Kano da Jami'ar Sule Lamido (SLU) ta jihar Jigawa.
ASUU ta gargdi gwamnatin tarayya
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga sabon yajin aiki kan gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan alawus din da ta yi alkawari.
ASUU ta bayyana cewa muddin Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta ci gaba da take alkawuran da ta dauka, to ba ta da wani zabi illa ta umarci mambobinta su fara yajin aiki.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da shi a watan Mayun da ya gabata.
Asali: Legit.ng