Minista Ya Fadi Abin da ke Bata Masa Rai game da Yan Kasa kan Gwamnatin Tinubu
- Ministan Ayyuka a Najeriya, David Umahi, ya bayyana bakin cikin da ke damunsa game da sukar gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya
- Umahi ya bayyana cewa Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 111 domin fara aikin babbar hanyar Akwanga zuwa Maiduguri
- Ya ce manyan ayyukan hanyoyi huɗu za su haɗa yankunan Najeriya shida, su ƙarfafa tsaro, kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Ayyuka, David Umahi, ya yi magana kan kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi a Najeriya baki daya musamman kan ayyukan alheri.
Umahi ya ce yana matuƙar baƙin ciki duk lokacin da ya ji mutane suna cin mutuncin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda abin takaici ne.

Source: Facebook
Umahi ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da aikin babbar hanyar Akwanga zuwa Maiduguri a Nasarawa, cewar rahoton Punch.
Umahi ya yaba da salon mulkin Tinubu
Umahi ya yabawa shugaban ƙasar saboda jajircewarsa wajen bunƙasa ababen more rayuwa, yana mai cewa mutum ne mai aiki fiye da yawan magana.
Ya kuma sanar da cewa Shugaba Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 111 domin fara matakin farko na aikin.
Tsohon gwamnan ya ce kamfanonin da aka ba kwangilar za su fara aikin gini a zahiri cikin mako guda.
A cewarsa, babbar hanyar Akwanga zuwa Maiduguri na ɗaya daga cikin manyan ayyukan hanyoyi huɗu da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Ministan ya lissafo sauran ayyukan da suka haɗa da hanyar Lagos zuwa Calabar, hanyar Cross River zuwa Ebonyi, Benue, Nasarawa da Abuja, da kuma babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.

Source: Facebook
Muhimmancin manyan hanyoyi da ake yi
Umahi ya ce waɗannan manyan hanyoyi za su rage lokacin tafiye-tafiye, su ƙara bunƙasa kasuwanci tsakanin jihohi, su inganta tsaro tare da haɓaka tattalin arzikin yankuna daban-daban, cewar Tribune.
Ya kuma kare matakin gwamnatin tarayya na amfani da fasahar kankare mai ƙarfi wajen gina manyan hanyoyi, yana mai cewa tana da ɗorewa fiye da hanyoyin kwalta kuma ba ta buƙatar yawan gyare-gyare.
Da yake yabawa Tinubu, Umahi ya bayyana ayyukan hanyoyin da ake gudanarwa a matsayin waɗanda ba a taɓa ganin irinsu ba a tarihin Najeriya.
Umahi ya ce yana da sa'ar yin aiki ƙarƙashin shugaban ƙasa mai mayar da hankali kan gina ababen more rayuwa, wanda yake da ƙarfin hali kuma ke da burin ciyar da Najeriya gaba.
'Abin da Musulmi za su yi ga Tinubu' - Minista
Mun ba ku labarin cewa ministan ayyukan tarayya, Sanata David Umahi, ya yi buɗa baki tare da al'ummar Musulmai a gidansa da ke jihar Ebonyi.
David Umahi ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga al'ummar Musulmai su marawa shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027.
Tsohon gwamnan na jihar Ebonyi ya bayyana shugaba Bola Tinubu yana da kyakkyawar manufa kan ci gaban Najeriya wanda daman shi ne babban abin da ke gabansa.
Asali: Legit.ng

