Soke Rajistar NDC: IPAC Ta Yi Zargin ana Shirin Birne Dimokuradiyya a Najeriya

Soke Rajistar NDC: IPAC Ta Yi Zargin ana Shirin Birne Dimokuradiyya a Najeriya

  • Kungiyar Gamayyar Jam’iyyu, IPAC ta bayyana cewa akwai kura a shirin da ake yi na soke rajistar wasu daga cikin jam'iyyun adawa
  • Majalisar ta bukaci Hukumar kula da tsagin shari'a da ya tashi tsaye wajen tabbatar alkalai sun kasance masu zaman kansu ba 'yan amshin shata ba
  • IPAC ta yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin kafa jam'iyya ɗaya ta hanyar kotu ko wasu hukumomi ba zai yi nasara ba, duk da barazanarsa ga dimokuradiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar Gamayyar Jam’iyyu, IPAC ta bayyana cewa soke rajistar jam'iyyun siyasa ta hanyar hukuncin kotu na iya zama babbar barazana ga tsarin dimokuraɗiyya.

Ya bayyana cewa bayan tumurmushe dimokuradiyya da jam'iyyun siyasa, wannan karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana batun 2027, gwamna Sule ya tono sirrrin APC kan nasarar da ta ke samu

IPAC ta yi magana kan hukuncin kotu game da rajistar NDC
Wasu daga cikin yan jam'iyyar hamayya ta NDC a Abuja Hoto; Henry Seriake Dickson
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na IPAC, Martins Egbeola, ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba 1 ga watan Yuli, 2026.

NDC: IPAC ta yi magana hukuncin kotu

Jaridar Daily Post ta kawo labarin cewa yayin da yake mayar da martani kan wasu hukunce-hukuncen kotu da suka shafi wasu jam'iyyun siyasa, daga ciki har da jam'iyyar NDC.

A cewarsa, irin waɗannan hukunce-hukuncen suna haifar da damuwa kan makomar dimokuraɗiyya mai bai wa jam'iyyu daban-daban damar fafatawa.

Ya ce hukunce-hukuncen da suka umarci a soke rajistar jam'iyyu biyar a baya, tare da sabon hukuncin da ya shafi NDC, na iya rage damar dimokuraɗiyya a ƙasar idan aka ci gaba da aiwatar da irin wannan tsari.

IPAC ta bukaci a kare 'yancin kotuna

Egbeola ya jaddada cewa, ko da kuwa akwai hujjojin shari'a a kowace ƙara, tasirin irin waɗannan hukunce-hukuncen gaba ɗaya na iya raunana ruhin dimokuraɗiyyar kundin tsarin mulki da kuma tsarin jam'iyyu da dama da Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Takarar Atiku Abubakar 'tana ƙasa tana dabo'

IPAC ta ce taba NDC barazana ce ga sauran jam'iyyu da siyasar Najeriya
Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Haka kuma ya bukaci Majalisar Kula da Harkokin Shari'a ta Ƙasa (NJC) ta tabbatar da cewa alkalai sun kasance masu zaman kansu, marasa son rai, kuma masu bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Ya ƙara da cewa:

"Bangaren shari'a shi ne fata na ƙarshe ga talaka, kuma bai kamata a rika kallonsa a matsayin kayan aikin 'yan siyasa ba."

Uba Sani ya magantu kan NDC

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya aika da sako ga 'yan siyasar da ke kushe bangaren shari'a na Najeriya, musamman bayan hkuncin da ya danganci jam'iyyun adawa.

Gwamna Uba Sani ya tunatar da cewa bai kamata ana siyasantar da hukunce-hukuncen da kotuna ke yankew a ba saboda kawai ba a samu yadda ake so ba, duk da cewa a baya an mori hukunce-hukuncen.

Gwamnan ya tunatar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar hamayya ta NDC, Mista Peter Obi a kan yadda ya baya ya taba cin gajiyar hukuncin kotu a lokacin da ya ke gwamna a jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng