2027: Kotu Ta Karbi Bukatar INEC a Shari'ar da Aka Nemi Soke Takarar Sheikh Pantami a Gombe

2027: Kotu Ta Karbi Bukatar INEC a Shari'ar da Aka Nemi Soke Takarar Sheikh Pantami a Gombe

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Gombe ta fara sauraron ƙarar da Khamisu Mailantarki ya shigar kan takarar Farfesa Isa Pantami
  • Mailantarki ya yi zargin cewa Sheikh Pantami bai shiga zaɓen fitar da gwani ko sayen fom ba kafin samun tikitin takarar gwamna na PDP
  • Kotu ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Yulin 2026 domin bai wa kowane bangare damar kare kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke zama a birnin Gombe ta sake zama domin sauraron karar da Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki ya shigar gabant, inda yake kalubalantar tikitin takarar gwamna na jam'iyyar PDP.

A cikin karar tasa, Mailantarki yana neman kotu ta tantance sahihancin takarar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda aka ba takarar gwamnan Jihar Gombe a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Ana neman yi wa Gwamna Inuwa karan tsaye kan takarar sanata a Gombe

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ke jagorantar sauraron shari’ar, kamar yadda jaridar Aminiya Hausa ta rahoto.

Mailantarki ya shigar da karar Pantami

Mailantarki ya lissafo Jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Pantami da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin wadanda yake kara.

A cikin ƙarar da ya shigar, Mailantarki ya yi zargin cewa an ba Pantami tikitin takarar gwamna ne ta hanyar maslaha maimakon gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani kamar yadda dokar zabe ta tanada.

Ya kuma yi iƙirarin cewa jam’iyyar PDP ba ta amince da wata yarjejeniyar maslaha da ta ba Pantami tikitin takarar ba.

A cewar Mailantarki, Farfesa Pantami ba ya ma cikin jerin mutanen da suka nemi tikitin takarar gwamnan tun farko, domin kuwa bai sayi fom din tsayawa takara ba, sannan bai halarci tantance 'yan takara da jam'iyyar ta gudanar ba.

Ya nemi a soke takarar Pantami

Mailantarki ya kara da cewa, Pantami ya fara yunkurin neman tikitin takarar gwamna ne a karkashin inuwar jam'iyyar APC, kuma a daidai lokacin da jam'iyyar PDP ta amince da tsarin sulhu ko maslaha, bai ma kammala zama cikakken dan PDP din ba.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar N400m: Atiku ya bukaci Tinubu ya kori shugaban ma'aikatansa

Bisa ga wadannan dalilai, ya bukaci kotun da ta soke takarar ta Pantami a matsayin dan takarar gwamnan PDP, sannan ta ba da umarnin gaggauta cire sunansa daga cikin jerin 'yan takarar gwamna na jam'iyyar a Jihar Gombe.

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami yayin da ya daga shaidar takara da ya karba daga PDP Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

INEC ta nemi ƙarin lokaci

A zaman kotun, lauyan INEC, Barista Ayuba Peter, ya bayyana cewa hukumar ta samu umarnin kare kanta ne kwanan nan.

Ya roƙi kotu ta ba ta ƙarin lokaci domin shigar da amsar ƙarar tare da bai wa sauran ɓangarorin shari’ar kwafinta.

Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta amince da buƙatar, sannan ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 9 ga Yulin 2026.

Pantami ya karbi shaidar takara

A baya, kun ji cewa tsagin PDP da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba Farfesa Isa Ali Pantami takardar shaidar zama ɗan takarar gwamnan Gombe a zaben 2027.

Pantami ya karbi takardar ne yayin taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) da kuma rantsar da sababbin mambobin NEC na jam’iyyar a hedkwatar PDP da ke birnin Abuja.

A yayin taron, jam’iyyar PDP ta mika takardun shaidar takara ga wasu daga cikin ‘yan takarar gwamna da aka amince da su tare da wallafa sunayensu a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262