Allahu Akhbar: Babban Likita Ya Rasu Mintuna 15 bayan Ya Zo Duba Marasa Lafiya a Kano
- Wani babban likita kwararre ya rasu bayan ya fadi a Asibitin Arewa Surgery da ke unguwar Hotoro a jihar Kano
- Rahotanni sun nuna cewa marasa lafiya, wadanda mafi yawansu tsofaffi ne sun shafe sa'o'i suna jiransa kafin isowarsa domin duba su
- An garzaya da shi sashen gaggawa, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa cikin mintuna 15 bayan isowarsa asibitin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wani kwararren likitan da ke aiki a Jihar Kano ya rasu bayan ya fadi jim kadan bayan ya isa Asibitin Arewa Surgery da ke Hotoro, inda ya je domin duba marasa lafiyar da suka dade suna jiransa.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da ta wuce bayan an bukaci marigayin, wanda aka bayyana sunansa da Dokta Ibrahim, ya maye gurbin wani likitan da ya kasa halartar aikinsa na yamma.

Kara karanta wannan
DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya

Source: Original
Hadimin gwamna ya kai mahaifiyarsa
Daily Trust ta ruwaito cewa wani hadimin Gwamnan jihar Jigawa, Suleiman Harbo, wanda ya bayyana abin da ya faru, ya ce yana cikin mutanen da suka kai 'yan uwansu asibitin lokacin da lamarin ya auku.
Suleiman ya ce ya kai mahaifiyarsa tsohuwa asibitin da misalin karfe 5:00 na yamma domin ganin likita.
Ya ce ma'aikatan asibitin sun sanar da su cewa likitan da aka tsara ba zai zo ba, sannan suka ba su shawarar su jira Dr. Ibrahim.
A cewarsa, marasa lafiya kusan shida, mafi yawansu masu shekaru sama da 80, sun ci gaba da jiran likitan.
Dr. Ibrahim ya rasu cikin mintuna 5
Suleiman Harbo ya ce bayan isowarsa asibitin, Dr. Ibrahim ya fara jin jiri nan take bayan ya fito daga motarsa.
An garzaya da shi sashen kula da marasa lafiya na gaggawa, inda wasu manyan likitoci suka yi kokarin ceto rayuwarsa, amma cikin mintuna 15 aka tabbatar da rasuwarsa.
A sanarwar da ya wallafa a shafin Facebook, hadimin gwamnan ya ce:
"Abin tausayi shi ne, duk marasa lafiyar da suke jiransa sun haura shekara 80, sannan kusan manyan likitoci biyar ne suka yi kokarin ceto shi, amma daga karshe suka fashe da kuka."
Marasa lafiya sun masa addu'a
Suleiman Harbo ya ce mahaifiyarsa ba ta san abin da ya faru ba da farko, har ta tambaye shi ko likitan ya iso amma kafin ya ba ta amsa, wani mara lafiya ya sanar da ita cewa likitan da suke jira ya rasu.
Da jin haka sai ta ce:
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ashe shi ne likitan da aka garzaya da shi ciki? Allah Ya jikansa. Mu dai mu koma gida, ni ma na samu sauki."

Source: Facebook
Kalmar da likitan ya fada ta ƙarshe
Ya kuma bayyana cewa mutanen da suka kasance tare da likitan a lokacin karshe sun ce kalmar da aka ji daga bakinsa ita ce: "La ilaha illallah."

Kara karanta wannan
Allah Ya ceci wani mutumi da matarsa ta lallaba za ta yanka masa wuya yana barci a Katsina
Harbo ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya jikansa da rahama, Ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus.
An sauya sunan asibiti a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sunan Babban Asibitin Dawakin Tofa zuwa Dr Mahmoud Baffa Yola General Hospital.
Gwamna Abba ya yi haka ne domin karrama marigayi Mahmoud Baffa Yola, dattijon kasa da ya yi fice wajen hidimtawa al’umma da ci gaban jihar Kano.
Ya kuma umarci Ma’aikatar Lafiya ta Kano da ta fara aiwatar da gyaran asibitin da gwamnatin ta amince da shi tun da farko, tare da tantance kayan aikin lafiya da ake bukata.
Asali: Legit.ng
