Majalisa ta Fara Binciken Yawaitar Hadurran Jirgin Kasa a Najeriya

Majalisa ta Fara Binciken Yawaitar Hadurran Jirgin Kasa a Najeriya

  • Majalisar wakilai ta ce za ta bincika domin gano matsalar da ke addabar bangaren sufurin jirgin kasa a Najeriya domin ita ce hanya mafi saukin zirga-zirga
  • Wannan ya biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar Makarfi-Kudan na jihar Kaduna, Umar Ajilo ya gabatar a kan a duba halin da jirgin Abuja-Kaduna yake ciki
  • Rahotanni sun bayyana cewa a cikin mako biyu, jirgin ya zame sau biyu daga kan layin dogon da ya ke tafiya a kai, kan haka ne aka gayyaci ministan sufuri Sa'id Alkali

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Majalisar wakilan Najeriya ta dauki gabarar binciken musabbabin yawan matsala da jirgin kasan Abuja-Kaduna ke samu a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

"An maida rai ba komai ba," Atiku ya riga shugaban kasa ta'aziyyar kisan Katsina

Domin gano matsalar, majalisar ta gayyaci ministan sufuri, Sa’idu Alkali da ya warware mata halin da jirgin kasan ke ciki da ma sauran matsaloli.

Majalisa
Majalisa za ta binciki matsalolin bangaren sufurin jirgin kasa Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Vanguard News ta wallafa cewa haka kuma wakilan ‘yan Najeriya sun sha alwashin gano dalilan yawan kaucewa da jiragen kasar nan ke yi daga layin dogon da su ke kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa za ta gano matsalar jirgin kasa

'Dan majalisa mai wakiltar Makarfi-Kudan na jihar Kaduna, Umar Ajilo ya shaidawa majalisar wakilai cewa akwai bukatar a gano abubuwan da su ke jawo matsala a sufurin jirgin kasan Najeriya.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa dan majalisar na ganin sufurin jirgin kasa ne mafi rashin hatsari a duniya, saboda haka bai kamata a rika samun matsala ba.

'Yan majalisa za su gayyato Minista

A kudurin da ya gabatar, ya nemi a gaggauta bincika dalilan da su ka jawo jirgin kasan Abuja-Kaduna ya fice daga layin dogon da ya ke kai har sau biyu a cikin mako biyu.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa na neman mayar da ofishin mataimakin shugaban ƙasar Najeriya ya zama 2

Majalisar ta amince da kudurin, inda ta gayyaci ministan sufuri, Sa’idu Alkali ya bayyana gabanta domin amsa tambayoyi kan yawaitar matsalar.

Majalisa ta nemi kara wa'adin shugaban kasa

A baya mun kawo muku labarin cewa majalisar kasar na nemi tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasa a Najeriya zuwa shekaru shida maimakon hudu, kuma wa'adi guda.

'Yan majalisar sun nemi a yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima ta yadda za a sauya wa'adin mulkin zuwa guda daya, sannan ya bayar da damar karba-karba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel