Atiku Ya Karfafa Shirin Kifar da Tinubu, Ya Nada Sabon Mai Magana da Yawunsa
- Yayin da ake shirin 2027, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya naɗa Kenneth Okonkwo a matsayin mai magana da yawunsa
- A bayanin da ya yi bayan nada shi, Kenneth Okonkwo ya ce Atiku ya fi son tattaunawa da sasanci maimakon fushi idan aka samu sabani
- Bugu da kari, Okonkwo ya bayyana cewa an tattauna batun cigaban yankin Kudu maso Gabas a jam'iyyar ADC kafin ya karbi mukamin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCt, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya naɗa jigo a jam'iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, a matsayin mai magana da yawunsa.
Hakan na zuwa makonni kaɗan bayan ɗan siyasar wanda tsohon jarumin fina-finai ne ya soki ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Mai magana da yawun Atiku
Okonkwo ne ya sanar da naɗin a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis, inda ya gode wa Atiku bisa amincewar da ya nuna masa.
Ya ce:
“Ina gode wa Allah bisa naɗa ni da mai girma Atiku Abubakar ya yi a matsayin mai magana da yawunsa. Ina kuma gode masa saboda irin amincewar da ya nuna a gare ni.”
Okonkwo ya ce wannan naɗin ya nuna irin salon jagorancin Atiku, yana mai cewa maimakon ya fusata idan wani daga cikin na kusa da shi ya bayyana damuwa kan wani mataki da aka ɗauka, yakan fi zaɓar tattaunawa da sasanci.
Ya kuma bayyana cewa a yayin tattaunawa da Atiku da sauran shugabannin ADC, an tattauna muradun yankin Kudu maso Gabas tare da tabbatar da su duk da ƙalubalen da dokar zaɓe ta 2026 da kuma halin da ake ciki suka haifar.
Godiya ga manyan ADC
Bugu da kari, Okonkwo ya miƙa godiyarsa ga Dr Kashim Imam, tsohon Shugaban ADC Ralphs Nwosu da kuma babban hadimi na musamman ga Atiku, Dr Ekene Onwuka, saboda rawar da suka taka wajen ƙarfafa jam'iyyar gabanin zaɓen 2027.
Haka kuma ya gode wa iyalansa, masoyansa da abokansa bisa addu'o'i da goyon bayan da suka ba shi, yana mai roƙon Allah Ya ba shi hikima, ƙarfin hali, arziki da kariya domin sauke sabon nauyin da aka ɗaura masa.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa naɗin ya zo ne makonni kaɗan bayan da Okonkwo ya soki zaɓin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi.
An turawa INEC sunan Atiku
A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar ADC sanar da cewa ta mika wa hukumar zabe sunan Atiku Abubakar ta shafinta na yanar gizo.
Kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya ce matakin na da matukar muhimmanci.
Bugu da kari, Bolaji Abdullahi ya kara da cewa sun tura sunan dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi.
Asali: Legit.ng

