Bam Ya Tarwatse da Sojojin Najeriya a Hanyar zuwa Kai Dauki, An Rasa Rayuka

Bam Ya Tarwatse da Sojojin Najeriya a Hanyar zuwa Kai Dauki, An Rasa Rayuka

  • Dakarun Sojoji biyu sun rasu, yayin da guda daya ya jikkata bayan motarsu ta taka bam da ake zargin 'yan bindiga ne suka dasa
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a hanyar Tidibale zuwa Tagirke a karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato
  • Wannan shi ne karo na uku da aka samu tashin bam a gabashin jihar Sakkwato cikin kwanaki 11 kacal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Sojoji biyu sun rasu, yayin da wani ya samu raunuka bayan wani bam da ake zargin 'yan bindiga ne suka dasa ya fashe a safiyar jiya Laraba a Sakkwato.

Bayanai sun nuna cewa bam din ya tashi da motar dakarun sojoji a hanyar Tidibale zuwa Tagirke da ke karamar hukumar Isa a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Mutum 18 'yan asalin jihar Sakkwato sun mutu lokaci guda a hanyar dawowa daga Legas

Dakarun soji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: Nigerian Army
Source: Twitter

Majiyoyi sun shaidawa Daily Trust cewa sojojin, wadanda ke aiki a Sansanin Sojoji na Gaba (FOB) da ke Tidibale, suna kan hanyarsu ta kai dauki ga jami'an tsaro bayan samun rahoton cewa ana kai hari a garin Tagirke

Yadda motar sojoji ta taka bam

Wani mazaunin karamar hukumar Isa ya ce motar sojojin ta taka bam din ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin harin.

Ya ce sojoji biyu sun mutu nan take, yayin da wani soja mai suna Abubakar, wanda aka fi sani da Bukar, ya tsira da raunuka.

A cewarsa:

"Sojojin na kan hanyarsu ta kai dauki bayan samun rahoton hari lokacin da motarsu ta taka bam. Sojoji biyu sun rasu, yayin da guda daya ya jikkata."

Ko da yake garin Tagirke yana karkashin karamar hukumar Sabon Birni, fashewar bam din ta faru ne a yankin karamar hukumar Isa.

Harin bam na uku cikin kwanaki 11

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

Wannan hari ya zo ne kwanaki 11 kacal bayan wani bam ya kashe sojoji uku tare da jikkata wasu tara a Bargaja a ranar 20 ga Yuni, 2026.

Haka kuma, a ranar Lahadi da ta gabata, wani bam ya sake fashewa a hanyar Kurawa zuwa Sabon Birni, inda ya lalata wata mota da babur tare da jikkata matafiya da dama, ko da yake ba a samu mace-mace ba.

Jama'a sun nuna damuwa

Mazauna yankunan gabashin Sokoto sun bayyana cewa yawaitar dasa bama-bamai a kan hanyoyi ya kara jefa jama'a cikin fargaba, tare da sanya zirga-zirga cikin hadari ga fararen hula da jami'an tsaro.

Wani mazaunin garin Sabon Birni, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce amfani da irin wadannan bama-bamai na nuna sabon salo da kungiyoyin masu dauke da makamai suka fara amfani da shi.

Ya bukaci gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin dakile lamarin.

Yan bindiga sun kashe liman a Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe babban limamin kauyen Kuda-Kuda da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: 'Yan daba sun buɗe wa mutane wuta, sun harbi wani jigon APC a Osun

'Yan bindigan sun kashe malamin addinin wanda aka gano sunansa Liman Audu tare da wasu mutane uku, yayin da aka yi garkuwa da wasu mutane a harin.

'Yan bindigan sun rika harbe-harbe ba kaukautawa, suka kora dabbobi, tare da sanya mazauna garin tserewa domin tsira da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262