Gwamna da Wa’adinsa bai Kare ba, Tsofaffin Gwamnoni da Masu Ci da ke Takarar Sanata
- Da wasu tsofaffin gwamnonin jihohi za a fafata wajen neman kujerar Majalisar dattawan Najeriya a zabe mai zuwa
- Shi kan shi Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio tsohon gwamna ne kuma an ce akwai masu hangen mukaminsa
- Akwai gwamnoni hudu da ke kan karagar mulki wadanda suka samu tikitin takarar sanata, dukkansu a inuwar jam’iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa wato Jibrin Barau sun tabata ‘yan takarar sanatoci a zaben 2023.
Sauran shugabanni a majalisa ta 10 da suka samu tikiti sun kunshi Opeyemi Bamidele da Mohammed Monguno kuma sun karbi fam.

Source: Getty Images
Gwamnonin da za su iya zama sanatoci
The Nation ta ce gwamnoni da dama sun samu takarar sanata - Hope Uzodimma (Imo) da Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa) da Inuwa Yahaya (Gombe).
Shugaban gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara) shi ma zai nemi ya wakilci Kwara ta tsakiya a Majalisar dattawa a 2027.

Kara karanta wannan
Gwamna da ke takarar shugaban kasa ya runtuma kora, ya yi sauye sauye a gwamnatin Oyo
Abdullahi Sule, Dapo Abiodun da Mai Mala Buni sun daura aniyar zama sanatoci a shekarar badi.
Akwai rudani game da takarar AbdulRahman AbdulRazaq a Kwara ta tsakiya, akasin abin da za a gani a Arewacin Adamawa da Arewacin Gombe.
Shi ma Inuwa Yahaya zai gwabza ne da wani tsohon gwamnan – Ibrahim Hassan Dankwambo wanda tun 2010 yake majalisa a inuwar PDP.
Gwamna zai hakura da kujerarsa ya zama sanata?
Abin da ya fi jan hankali shi ne lamarin Hope Uzodimma wanda zai yi takara alhali wa’adinsa ba zai kare ba har lokacin da za a rantsar da majalisar.
‘Dan siyasar ba bako ba ne a majalisa domin kafin nasararsa ta sanadiyyar Kotun koli a shekarar 2020, ya yi shekaru takwas a Majalisar dattawa.
Idan ya ci zabe a Imo ta yamma, akwai yiwuwar zai yafe ragowar wa'adinsa na gwamna.
Tsofaffin gwamnoni za su nemi zama sanatoci
Akwai tsofaffin gwamnonin kasar nan da za su yi takarar Majalisar dattawan a zabe mai zuwa kamar yadda The Cable ta taba yin nazari a kan batun.
Mukhtar Ramalan Yero wanda ya mulki jihar Kaduna daga 2010 zuwa 2011 zai nemi sanatan Arewacin Kaduna a karkashin jam’iyyar APC.

Source: Getty Images
A baya Mukhtar Ramalan Yero ya yi ta kokarin koma wa kujerar gwamna a Kaduna, amma ko zaben tsaida gwani bai iya samu a jam’iyyarsa ba.
Shi ma Yahaya Bello da ya yi shekaru takwas yana mulki a jihar Kogi zai kara da su Natasha Akpoti-Uduaghan a Kogi ta tsakiya a zaben badi.
Jerin tsofaffin gwamnoni masu son zarcewa a majalisa
Ban da masu neman zuwa a karon farko, akwai tsofaffin gwamnoni kamar Godswill Akpabio, Aliyu Wamakko da Adams Oshiomhole da za su sake takara.
Sannan akwai Orji Uzor Kalu, Ifeanyi Okowa, Adamu Aliero, Simon Lalong, Ibrahim Shekarau da Abubakar Sani Bello dukkansu 'yan APC ne.
Wasu na ganin Adams Oshiomhole da Uzodinma za su hari kujerar shugaban majalisa, ana jita-jitar suna da burin gaje wurin Sanata Akpabio.
Oshiomhole da Uzodinma sun fito daga yankunan Kudu maso gabas da Kudu maso yammacin Najeriya, inda ake ganin shugaban majalisa zai fito.
APC ta canza 'yan takaran Majalisar tarayya
Dazu aka karanta cewa labari ya canza da aka nemi sunayen wasu ‘yan takaran APC aka rasa a sakamakon sauye-sauyen da jam'iyya ta yi.
Fusatattun masu neman takara sun gargadi APC game da canza sunayen wadanda har an fara ganin sun samu tikiti, zabe ya rage kawai a shiga.
Ta leko ta koma da sunayen ‘yan takaran APC suka canza farat daya kuma wannan ya shafi tsohon gwamnan Benuwai, Sanata Gabriel Suswam.
Asali: Legit.ng

