INEC Ta Bullo da Sauyi da Ya Saukaka wa Mutane Harkar Zabe daga cikin Daki
- INEC ta sanar da cewa yanzu mutum zai iya sauke katin zaben shin a PVC da kansa, a maimakon sai ya je ofishin hukuma
- Joash Amupitan ya yi bayanin kokarin da ake yi na ganin mutane sun iya yin rajistar PVC ba tare da ziyartar ofishin INEC ba
- Hukumar za ta fara bada damar sauke sabon PVC ne ga wanda katinsu ya bace ko ya lalace daga zaben gwamnan jihar Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya da ake kira INEC tana shirin fito da katin PVC da mutum zai iya sauke wa da kan shi.
Idan mutum ya rasa katin zaben shi na ainihi da hukumar ta ba shi ko kuma wani dalili ya sa PVC din ya bace, da kan sazai iya sauke wani.

Source: Getty Images
INEC: "Za a fara sauke PVC daga gida"
Shugaban hukumar zabe na kasa, Joash Amupitan ya yi maganar nan lokacin Darekta Janar na NOA ya ziyarce shi a cewar The Cable.
Lanre Issa-Onilu da ke jagorantar hukumar NOA mai wayar da kan jama’a ya zauna da Farfesa Joash Amupitan a hedikwatar INEC a Abuja.
Shugaban hukumar INEC ya ce wannan sabuwar fasaha tana cikin kokarin da ake yi na zamantar da harkar zabe kafin takarar da za a yi a 2027.
Daga duk inda suke, za a ba wanda ya saba yin zabe damar sauke katin shi na PVC daga kan na’ura.
Sai dai Joash Amupitan ya yi karin haske cewa wannan kofa ba a bude ta ke ga kowa ba, ban da wanda tun farko bai taba karbar katin PVC ba.
“Ba kowane PVC ne za a iya saukewa ba. Dole sai kana da katin ka na PVC kafin nan kuma dole sai idan ya bace, lalace ko ba za a iya karanta lambar da ke jikinsa ba,”
- Shugaban INEC
Daily Trust ta ce idan irin haka ta faru da mai katin zabe, sai ya sanar da INEC a hukumance domin ta fara shirin yadda zai sauke wani PVC na dabam.
Wata ka’ida da Amupitan ya fada ita ce, ya zama tilas a yi wannan kwanaki 90 gabanin shirya zabe.
INEC za ta kawo tsarin rajista daga gida
Hukumar ta INEC za ta fara yin gwajin wannan sabuwar fasaha ne daga zaben gwamnan da za a gudanar nan da ‘yan kwanaki, wato a watan Agusta.
Zuwa yanzu, Amupitan ya ce ana neman karkare fasahar da za ta ba ‘yan kasa damar kammala rajistar mallakar katin zabe ba tare da zuwa INEC ba.

Source: Getty Images
Ana so mutumin da shari’a ta ba damar yin zabe ya yi komai ko da bai san hanyar ofishin INEC ba.
Sabon shugaban na INEC ya shaida wa jama’a cewa yana fatan za a fara gwajin wannan fasaha da zarar hukumar ta kasa ta yi zama kuma ta amince da ita.

Kara karanta wannan
"Ba ka isa ba," Jigon ADC ya takawa Wike birki kan wanda zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027
Manufar duk yin wadannan abubuwa ba komai ba ce illa ganin babu wanda aka bari a baya wajen kada kuri’a domin zaben shugabannin da suke so.
An kawo manya-manyan sauyi a NYSC
Rahoton nan ya ce Gwamnatin tarayya ta kawo wasu canji da za a gani wajen yi wa kasa hidima bayan shekaru kimanin 50 da sojoji suka kafa hukumar.
Canjin za su bayyana tun daga garuruwan da ake zuwa da kwanakin da ake yi a sansanin NYSC da kuma karbe shugabancin NYSC daga hannun soja.
Har ila yau, za a yi la'akari da tsaro wajen tura matasa bautar kasar kuma za a dauki lokaci na musamman wajen koya masu karatun zamani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

