Shugaban INEC Ya Dauko Batun Satar Akwatin Zabe da Magudi gabanin 2027
- Hukumomi da sauran 'yan siyasa na ci gaba shirye-shiryen tunkarar babban zaben shekarar 2027 a tarayyar Najeriya
- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya yi maganar da za ta kwantar da hankalin 'yan Najeriya
- Farfesa Joash Ojo Amupitan ya bayyana cewa lokacin satar akwatin zabe da tafka magudi ya zama tarihi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan SAN, ya yi magana kan satar akwatin zabe.
Farfesa Amupitan ya bayyana cewa lokacin satar akwatin zabe da magudin sakamakon zabe da hannu ya wuce.

Source: Twitter
Me Amupitan ya ce kan satar akwatin zabe?
Jaridar Vanguard ta ce Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2026 a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar wayar da kan jama'a ta kasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, a wata ziyara da ya kai hedkwatar INEC.
Shugaban INEC ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa matakan kariya na fasaha na yanzu suna da karfin da za su kare kowace kuri’a da aka kada a babban zaben shekarar 2027.
Hukumomin biyu sun yi amfani da wannan dama domin zurfafa hadin gwiwa kan ilimantar da masu zabe gabanin zaben shekarar 2027.
Shugaban na INEC ya tuna cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Janairu, sannan na gwamnoni a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2027, rahoton Daily Post ya nuna hakan.
INEC za ta wayar da kan 'yan Najeriya
Ya ce dole ne hukumar ta fara gudanar da ayyukan wayar da kai ga ‘yan kasa cikin gaggawa, inda ya yi gargadin cewa rashin son fitowa jefa kuri'a da kuma yada labaran bogi na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga ingancin tsarin zabe.
“Muna bukatar mu koya masu dalilin da ya sa kuri'arsu ke da muhimmanci da kuma yadda sababbin matakanmu na shari'a da na fasaha ke kare zabin da suka yi."
"Dole ne mu kalli manomin karkara, matan kasuwa, da matashin birni da ya cire rai daga tsarin a ido mu bayyana musu da yaren da suke fahimta cewa, saboda tsarin fasahar da ake da shi a halin yanzu, zamanin sace akwatin zabe ko sake rubuta sakamako da hannu ya wuce.”

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Peter Obi ya mika bukatar da ta shafi Tinubu da sauran 'yan takara ga INEC
- Farfesa Joash Amupitan

Source: Facebook
INEC ta samu nasarori
Shugaban na INEC ya kuma amince da gagarumin nasarorin da aka samu lokacin zabubbukan Abuja na ranar 21 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamna na jihar Ekiti na ranar 20 ga watan Yunin 2026.
Farfesa Amupitan ya ce zabubbukan biyu sun fito da wata matsala ta rashin son fitowa jefa kuri'a da kuma rudani mai yawa a tsakanin masu zabe na birane game da raba rumfunan zabe da kuma canjin rajista.
INEC ta kawo matsala ga jam'iyyar NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kawo cikas ga shirin jam'iyyar NNPP dangane da zaben 2027.
Bayanai sun nuna cewa INEC ta hana jam'iyyar NNPP lambar shiga shafin shigar da bayanan 'yan takara har zuwa ranar Talata, 30 ga watan Yuni, 2026.
Sai dai, ba a bayyana dalilin hana jam'iyyar NNPP damar shigar da yan takararta a shafin hukumar zabe ta INEC ba.
Asali: Legit.ng
