Gwamna Ya Nuna Adawa da Kafa 'Yan Sandan Jihohi, Ya Fadi Dalilansa

Gwamna Ya Nuna Adawa da Kafa 'Yan Sandan Jihohi, Ya Fadi Dalilansa

  • Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba na da ra'ayin bai kamata a samar da ƴan sandan jihohi a ƙasar nan domin magance matsalar tsaro
  • Gwamnan ya nuna adawa da shirin ƙirƙiro ƴan sandan jihohin domin a cewarsa hukumomin tsaron da ake da su yanzu za su iya shawo kan matsalar
  • Ya bayyana cewa abin da hukumomin tsaron kawai suke buƙata shi ne ƙara samun goyon baya domin gudanar da ayyukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya nuna adawa da shirin ƙirƙiro ƴan sandan jihohi.

Gwamnan ya dage cewa hukumomin tsaron da ake da su a ƙasar nan na da ƙarfin magance ƙalubalen tsaro da ke addabar al’umma.

Kara karanta wannan

Sallah: Matawalle ya gwangwaje Zamfarawa da raguna, ya raba 390m daf da layyah

Gwamna Agbu Kefas na adawa da kafa 'yan sandan jihohi
Gwamna Agbu Kefas bai son a kafa 'yan sandan jihohi Hoto: @AgbuKefas
Asali: Twitter

Gwamna Kefas ya gana da kwamanda

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke mai kula da jihohin Nasarawa, Benue da Taraba, Janar L G. Leptang, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Agbu Kefas ya karɓi baƙuncin kwamandan ne a gidan gwamnati, da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar Talata.

Gwamna Agbu Kefas ya ce bayan ya yi aikin sojan Najeriya na wasu shekaru, ya san abin da sojoji da sauran jami’an tsaron Najeriya ke iya yi wajen tsaron ƙasa.

Me gwamnan ya ce kan ƴan sandan jihohi?

"Domin haka ne lokacin da mutane ke maganar samar da ƴan sandan jihohi sai na yi shiru. Na san ƙarfin sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaron ƙasar nan, na san ku babbar kadara ce ga Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya samo mafita ga gwamnati kan mafi karancin albashi

"Amma abin da kuke buƙata shi ne samun goyon bayan da ya dace da kuma samar da yanayin da za ku iya gudanar da ayyukanku."

- Agbu Kefas

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na haɗa kai da jihohin da ke makwabtaka da ita da Jamhuriyar Kamaru domin samar da hanyoyin shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Gargaɗin Shekarau kan ƴan sandan jihohi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tmtsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ƴan sandan jihohi.

Tsohon sanatan ya shawarci gwamnati kan hana ƴan sandan riƙe makamai bayan tabbatar da su domin daƙile abin zai je ya dawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel