Gaskiya Ta Fito, Tsarin Sabon Naira da Tsohon Gwamnan CBN Ya Yi Ba Irinsu Buhari Ya Amince Ba

Gaskiya Ta Fito, Tsarin Sabon Naira da Tsohon Gwamnan CBN Ya Yi Ba Irinsu Buhari Ya Amince Ba

  • Tsohon gwamnan CBN ya kara shiga matsala sabuwa yayin da bayanai ke ƙara fitowa kan tsarin sauya fasalin Naira
  • Tsohon daraktan harkokin kuɗi a CBN, Ahmed Umar, ya shaidawa kotun Abuja cewa Emefiele ya buga kalar sababbin kuɗin da ya ga dama ba wanda Buhari ya amince ba
  • Wannan na zuwa ne bayan EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a gaban kotu kan tuhume-tuhume huɗu a watan Mayu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon daraktan harkokin kuɗi a babban bankin Najeriya (CBN), Ahmed Umar, ya ci gaba da bayanin yadda aka yi canjin takardun Naira a mulkin Buhari.

Ahmed ya bayyana cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya buga kalar takardun Nairan da ya ƙirƙiro amma ba su shugaban ƙasa ya bayar da umarni ba.

Kara karanta wannan

Bankin CBN ya soke lasisin wasu manyan bankuna 4 a Najeriya? Gaskiya ta fito

Emefiele da Buhari.
Tsohon daraktan CBN ya bayar da shaida a gaban kotu kan canjin kuɗin Emefiele Hoto: @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

EFCC ta maka Godwin Emefiele a kotu

Idan ba ku manta ba a ranar 15 ga watan Mayu, 2024, hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Emefiele kan tuhume-tuhume huɗu a babbar kotun tarayya a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation ta kawo, ana zargin Emefiele da shure tanadin doka wajen aiwatar da tsarin canja takardun N200, N500 da N1000.

Haka nan ana tuhumarsa da yin gaban kansa wajen canjin kuɗin ba tare da sahalewar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da majalisar gudanarwa ta CBN ba.

Sai dai Mista Emefiele ya musanta aikata ko ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa, inda kotu ta bayar da belinsa kan N300m.

Yadda Emefiele ya shure tsarin Buhari

Da yake bayar da shaida a kotu, Ahmed Umar ya ce zanen da ke jikin kalar kuɗin da Buhari ya amince ya sha bamban da kalar da Emefiele ya sa aka buga.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan tsige ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC

"Tsarin sabon kuɗin da Buhari ya amince da shi yana da lambar QR Kod amma kuɗin da ke yawo a yanzu wanda Emefiele ya kirkiro ba su da shi.
"Haka nan an amince a sa hoto a ɓangaren dama amma CBN ya buga a hagu kuma tsarin lambobin jikin takardun kuɗin ya sha bambam da yadda shugaban ƙasa ya bayar da umarni."

Kotu ta kwace kadarorin Emefiele

A wani rahoton kuma kotu ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace wasu manyan kadarorin maƙudan kuɗi na tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya mai zama a Legas ne ya bayar da wannan umarnin ranar Laraba, 5 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel