Sarki Bamalli Ya Karyata Cewa Alakar Jini Ta Jawo El Rufai Ya Nada Shi Sarkin Zazzau

Sarki Bamalli Ya Karyata Cewa Alakar Jini Ta Jawo El Rufai Ya Nada Shi Sarkin Zazzau

  • Akwai dangantakar jini tsakanin Ahmad Nuhu Bammalo da Nasir El-Rufai, dukkansu sun fito ne daga gidan Mallawa
  • Sarki Bamalli ya karyata cewa alakar ta ba shi sarauta, ya ce ya biya kudin jirgi $9,000 da Shehu Idris ya rasu a 2020
  • Ya ce tun farko bai yi sha'awar shiga takarar neman sarautar Zazzau ba har sai da mutane suka matsa masa lamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli ya tabo tarihi da yadda ya samu sarauta bayan Alhaji Shehu Idris ya cika.

Mai martaba Sarkin ya rusa wasu ikirari da ake yi game da rawar da Nasir El-Rufai ya taka wajen samun sarautarsa a 2020.

Nasir El-Rufai
Sarki Ahmad Nuhu Bamalli a fadar Zazzau da Nasir El-Rufai ranar rantsar da sabon gwamna Hoto: Masoyin Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya shaida wa Daily Trust wasu abubuwa a kan sarautarsa gabanin cikarsa shekaru shida.

Sarkin ya ce ana daukar abubuwa ba daidai ba game da rawar da gwamnatin Nasir El-Rufai ta taka a wajen nada shi sarki.

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari ya fadi sirri da ya kama aikin tallar Tinubu babu kama hannun yaro

Alakar jini tsakanin Sarkin Zazzau da Nasir El-Rufai

Mai martaban ya tabbatar da cewa akwai alaka ta jini tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Kaduna.

Ahmed Nuhu Bamalli ya ce Malam El-Rufai da mahaifinsa ‘yanuwa ne, hakan ya sa sarki ya zama kamar kawu a wajen shi a danginsu.

Amma duk da haka ya ce bai kamata a fassara wannan dangantaka da cewa saboda ita aka amince da nadin shi a matsayin sarki ba.

Sarki Bamalli ya bayyana cewa shi da Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen iyaye suke wajen El-Rufai.

Shehu Idris ya rasu, sarki yana Thailand

A watan Oktoba mai zuwan nan na 2026, basaraken zai cika shekaru shida da gadon sarauta bayan rasuwar Shehu Idris.

Lokacin da Mai martaba Shehu Idris ya cika a asibiti a Kaduna, Ahmad Bamalli yana aikin jakadancin Najeriya a kasar Thailand.

Dole ya yi gaggawar dawo wa gida sa’ilin da duniya ta ke fama da annobar cutar COVID-19.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya ji dadin kokarin Uba Sani, ya fadi wahalar da sarakuna ke ciki

Saboda alakar jini gwamnatin El-Rufai ta nada shi sarki?

Ya ce sai da ya kashe $9000 a kudin jirgin sama domin ya dawo Najeriya tare da mai dakinsa da kuma ‘ya ‘yansa mata biyu.

Wannan ya karyata zancen da ake yi cewa El-Rufai ne ya turo jirgi a dauko sa, ya ce har yau yana da risitin tikitin jirgin saman.

Ya ce sai da ya iso filin jirgi ne a Abuja sai wani hadimin El-Rufai ya gan shi, ya sanar da gwamnan game da isowarsa Najeriya.

Daga nan sai gwamnatin Kaduna ta bada motoci a kai shi gidan danginsu a Zariya domin motocinsa ba su iya daukar shi ba.

Sarkin ya ce da farko bai yi niyyar neman sarautar ba, amma da aka matsa masa lamba sai ya jarraba kuma kaddara ta ba shi.

Sarki Ahmad Nuhu Bamalli
Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli a wajen wani taro Hoto: Masoyin Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli
Source: Facebook

Yadda El-Rufai ya soke zaben sarkin Zazzau

An ji labarin yadda Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya soke zaɓen farko da masu zaɓen Sarkin Zazzau suka gudanar.

Kara karanta wannan

'Wataƙila malamansa suka hana shi', Baba Ahmad kan Kashim da ƙin sa hular Tinubu

Sakamakon wannan umarni, masu zaɓen sarki sun sake zama domin yin la'akari da dukkanin ƴan takaran masarautar mai tarihi.

Wannan matakin ya ba wa waɗanda aka cire, da suka haɗa da Bunu Zazzau da Sarkin Dajin Zazzau damar sake shiga takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng