'Yan Damfara Sun Gudu da Miliyoyin Kudin da 'Yan Najeriya Suka Tura a PXES
- ’Yan Najeriya da suka zuba miliyoyin Naira a wani tsarin saka jari na yanar gizo mai suna PXES sun shiga rudani bayan daina biyan kuɗin da aka yi musu alkawari
- Masu saka jari sun kasa cire kuɗinsu bayan tsarin ya daina aiki a farkon watan Satumba, yayin da wasu suka kasa samun damar tuntubar masu gudanar da shi
- Lamarin ya haifar da fushi, inda wasu masu zuba jari suka kutsa ofisoshin PXES tare da kwashe kayayyaki a jihohin Adamawa da Kogi domin ƙoƙarin kwato kudinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – ’Yan Najeriya da suka saka kuɗi a wani tsarin saka jari na yanar gizo mai suna PXES na fuskantar asarar kuɗi bayan daina biyan kuɗin da aka yi musu alkawari.

Kara karanta wannan
Bayanai sun fito: An ji abubuwan da suka faru da Ɗan Shagamu kafin a kashe shi a Kano
Rahoto ya nuna cewa tsarin ya daina biyan mahalarta tun farkon watan Satumban 2026, inda wasu suka saka dubban Naira, yayin da wasu kuma suka zuba miliyoyin Naira.

Source: Facebook
An yaudari jama'a da batun riba
Rahoton Vanguard ya nuna cewa PXES ya jawo masu zuba jari ne ta hanyar alkawarin samun riba mai yawa a kullum.
An ce an yi wa wasu alkawarin dawowar kashi 25 zuwa 50 cikin 100, yayin da wasu suke fatan samun kashi 120 cikin 100 na abin da suka zuba.
Sai dai Punch ta ce ba ta iya tabbatar da sahihancin dukkan rahotannin da aka bayar kan ribar da tsarin ya yi alkawari ba.
Korafi a Adamawa da Kogi
A jihohin Adamawa da Kogi, masu zuba jari da suka kasa cire kuɗinsu sun kai farmaki ofisoshin PXES.
Bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna wasu mutane suna kwashe kujeru, tebura da wasu kayayyaki daga ofishin kamfanin da ke Yola.
Haka kuma, an ga makamancin wannan lamari a ofishin PXES da ke Kabba, inda aka ce masu zuba jari sun kasa samun bayanai kan makomar kuɗinsu.
Wani bidiyo ya nuna wani mutum da aka ce ya saka kusan N209,000 yana kuka tare da bayyana damuwarsa kan rashin samun kuɗinsa.

Source: Original
Yadda aka cuci mutane
Wata mai saka jari, Bunmi Awodipe, ta ce ƙawayenta uku ne suka ƙarfafa mata gwiwar shiga PXES bayan sun nuna mata shaidar cewa suna karɓar kuɗin da tsarin ya biya su.
Awodipe ta ce ta saka N200,000, inda ta fara karɓar N7,000 a mako, amma an biya ta na tsawon mako uku kacal.
Ta ce lokacin da ta je ofishin kamfanin a makon da ya gabata, ta tarar an kulle wurin kuma an kwashe kayayyakin da ke ciki.
Wani mai saka jari, Deji Mulero, ya ce wani kwastomansa ne ya gabatar masa da tsarin a ranar 4 ga Satumba.
Mulero ya ce ya yi rajista da N65,000, amma tsarin ya daina aiki a ranar Juma’ar da ya shiga.
Wani mai suna Wale ya ce ya saka N207,000, kuma kuɗin da ya tara a asusunsa ya kusan kai N600,000 kafin tsarin ya daina aiki.”
Za a fara ba dalibai data
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ɗaliban Najeriya za su fara samun data kyauta har 100MB a kowace rana daga ranar 1 ga Oktoba 2026.
An ce shirin zai bai wa ɗalibai damar shiga wasu shafukan ilimi da dandalin koyon karatu na zamani da aka amince da su a hukumance.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, za ta aiwatar da shirin tare da kamfanonin sadarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, inda za a fara da ɗaliban manyan makarantu.
Asali: Legit.ng

