Da duminsa: El_rufai ya sanar da sabon Sarkin Zazzau

Da duminsa: El_rufai ya sanar da sabon Sarkin Zazzau

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana sabon Sarkin Zazzau

- Kamar yadda wallafarsa ta shafinsa na Twitter ya bayyana, Ahmed Nuhu Bamalli ne sabon Sarkin

- Ambasadan ya maye gurbin Marigayi Dakta Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba

Labari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng shine sanarwar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na sabon Sarkin Zazzau.

Kamar yadda Gwamnan jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Da duminsa: El_rufai ya sanar da sabon Sarkin Zazzau
Da duminsa: El_rufai ya sanar da sabon Sarkin Zazzau. Hoto daga @GovKaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Auren Hausawa: Dukkan abinda ya kamata a sani daga nema zuwa samun auren

Ya gaji marigayi mai martaba, Alhaji Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a karagar mulkin.

KU KARANTA: Yadda Faisal Maina ya yi gaba da gaba da mutuwa a Abuja

Kamar yadda takardar ta bayyana, "Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya amince da nadin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.

"Ya maye gurbin marigayi Alhaji Dakta Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a kan karagar mulki.

"Alhaji Ahmed Bamalli shine Sarki na farko daga gidan Mallawa a cikin shekaru 100 tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Dan Sidi a 1920."

A wani labari na daban, Gwamnatin jihar Kaduna ba za ta yi amfani da rahoton da majalisar nadin sarki na masarautar Zazzau ta kai mata ba domin cike gurbin sarkin Zazzau, wata majiya da ta san kan lamrin ta tabbatar wa da Premium Times.

Wannan hukuncin ya dawo da Ahmed Bamalli, wanda aka tabbatar da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ke so a cikin masu zawarcin karagar mulkin.

Premium Times ta gano cewa, gwamnan ya yanke wannan hukuncin bayan zargin da yayi an bai wa wasu daga cikin 'yan majalisar cin hanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng