Bayanai Sun Fito: An Ji Abubuwan da Suka Faru da Dan Shagamu kafin a Kashe Shi a Kano

Bayanai Sun Fito: An Ji Abubuwan da Suka Faru da Dan Shagamu kafin a Kashe Shi a Kano

  • Ƙarin bayanai sun ci gaba da fitowa kan kisan Ibrahim Khalil Dan Shagamu, wanda aka yanka a gidansa a jihar Kano
  • Iyalansa sun ce wasu mutanen da ba a gano ko su waye ba ne suka kutsa gidansa suka kashe shi cikin dare
  • Wasu mazauna yankin na zargin cewa kisan na da alaƙa da daba, yayin da wasu ke danganta shi da kalamansa a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Bayanai na ci gaba da kara fitowa kan abubuwan da suka kai ga mutuwar Ibrahim Khalil Dan Shagamu, wani mai sharhi a kafafen sada zumunta da aka yanka a gidansa a Kano ranar Laraba.

’Yan uwansa sun ce wasu mutane da har yanzu ba a gano ko su waye ba ne suka kai masa hari bayan sun kutsa gidansa, inda suka kashe shi a tsakiyar dare.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya shiga maganar kashe Dan Shagamu a Kano, ya yi kira ga hukuma

Dan Shagamu.
Fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa da zamantakewa, Ibrahim Khalil Danshagamu Hoto: Ibrahim Khalil Danshagamu
Source: Twitter

Leadership ta rahoto cewa Dan Shagamu mai shekaru 54 ya rasu ya bar ’ya’ya shida, kuma an birne shi cikin kuka da tambayoyi da dama kan abubuwan da suka dabaibaye mummunan mutuwarsa.

Kalaman Dan Shagamu a Intanet

Bincike cikin sauri a shafukan sada zumuntansa ya nuna cewa Dan Shagamu ya kasance yana yawan wallafa bidiyoyin da yake ɗaukar kansa yana yin sharhi kan batutuwa daban-daban.

A cikin bidiyoyinsa, ya kasance yana sukar kusan kowa, daga ’yan siyasa, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin addini masu saɓani da shi har zuwa maƙwabtansa.

A cewar wasu manazarta, wannan na iya sanya kowanne daga cikin rukunin mutanen da ya taɓa suka ya zama wanda ake iya zargi da hannu a kisan nasa.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa baya ga abin da jama’a suka sani, ana zargin cewa wataƙila ya shiga cikin wani abu da ya sa maƙwabtansa suka fara zarginsa.

Kara karanta wannan

Ado Gwanja ya yi magana ana cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani

Abubuwan da duka faru da Dan Shagamu

Majiyar ta ce har da wani labarin da ya taɓa bayarwa a cikin ɗaya daga cikin bidiyonsa, inda ya yi zargin cewa an yi masa barazanar kisa sakamakon wata arangama da wani ƙaramin yaro.

Ta ce:

“Ba zai yiwu kowa a yankin ya juya wa mutum baya ba sai dai idan akwai wani abu da ke ɓoye. Yana da kyakkyawar alaƙa da ƙananan yara da ke yawan bin sa, lamarin da ya sa mutane ke zargin cewa wataƙila wannan alaƙar ba ta da kyau."
“Amma babu wanda ya iya tabbatar da irin alaƙar da ke tsakaninsa da su. Haka kuma yana rayuwa shi kaɗai a gidansa bayan ya rabu da matarsa. Ya tura ’ya’yansa shida su koma gidan kakanninsu bayan ya yi zargin cewa ana yi masa barazanar kisa."

Majiyar ta kuma ce rayuwar marigayi Dan Shagamu ta kasance cikin wani yanayi na saɓani, domin yana bayyana ra’ayinsa sosai a kafafen sada zumunta, amma a rayuwa ta zahiri mutum ne shiru-shiru kuma mai ƙarancin abokai.

Kara karanta wannan

'Yan uwan Dan Shagamu da aka kashe a Kano sun bayyana wani sirri kafin mutuwarsa

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta kuma yi zargin cewa yadda yake mu’amala da mutane ya nuna cewa yana da matsalar ɗabi’a.

“Ya yi zargin ana yi masa barazanar kisa a lokuta da dama ba tare da ya ambaci sunaye ba, kuma duk lokacin da aka tambaye shi ya bayyana sunayen waɗanda suke yi masa barazanar, ba ya yi,” in ji majiyar.

Iyalan Dan Shagamu sun nemi adalci

Kun ji cewa babban ɗan marigayi Ibrahim Khalil Dan Shagamu, Ammar Ibrahim Dan Shagamu, ya buƙaci a yi wa mahaifinsa adalci.

Ammar ya yi gargaɗin kada a danganta kisan da siyasa ba tare da cikakken bincike ba, amma ya buƙaci a gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262