Abdulaziz Yari Ya Fadi Yadda Ya Zama Sarkin Yakin Zaben Tinubu cikin Dubunnan 'Yan APC

Abdulaziz Yari Ya Fadi Yadda Ya Zama Sarkin Yakin Zaben Tinubu cikin Dubunnan 'Yan APC

  • Abdul’aziz Yari Abubakar ya kaddamar da shirin tallata nasarorin Mai girma shugaba Bola Tinubu ga al'umma
  • A matsayin Darekta janar na babban zaben 2027, tsohon gwamnan ya kama aikin kamfe daga Zamfara
  • Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar yana so Tinubu da Kashim Shettima su sake lashe zaben shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Abdul’aziz Yari Abubakar ya koma gida domin fara aikin da aka ba shi na Darekta janar na yakin zaben Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar yayi bayanin rawar da zai taka wajen yakin neman tazarce da kuma kokarin gwamnati mai-ci.

Tinubu
Magoya bayan APC a Abia da Abdulaziz Yari a Abuja Hoto: Tinubu Support Group/Bashir Ahmaad
Source: Facebook

Ya aka yi Abdul’aziz Yari ya zama darektan kamfe?

Daily Trust ta rahoto Abdul’aziz Yari Abubakar yana cewa tun farko Allah ne ya zabo shi ya zama Darekta Janar na kamfen 2027.

Tsohon gwamnan ya yi wannan zance ne a garin Gusau, babban birnin Zamfara lokacin da ya gana da masu ruwa da tsakin APC.

Kara karanta wannan

2027: Sanata Yari ya yanke hukunci kan wanda ya cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi

Abdulaziz Yari ya ce duk da aikin shi yana bukatar yawo a fadin Najeriya domin tallata Bola Tinubu, ya zabi ya fara ne daga gida.

Yari ya dauko tallar Tinubu daga mahaifarsa

‘Dan siyasar ya ga bukatar ya bude da nema wa shugaban kasar goyon baya daga Zamfara, jihar da ya fito har ya zama gwamna.

"Wannan gida na ne. Saboda haka duk abin da za mu yi, dole a yi nasara. Muna bukatar mu hada-kai…"

- Abdul’aziz Yari

Sanata Yari ya zauna da shugabannin APC na mazabu da kananan hukumomi da kuma wadanda ke matakin reshen jiha a Zamfara.

Ya fada masu cewa idan ana so ya yi nasara a 2027, ya zama dole duka ‘yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki su bada gudumuwarsu.

Darekta Janar din yake cewa Ubangiji ya damka masa wannan amana lokacin da ake da dubban mutanen da za su iya rike kujerar.

“Allah ya zabe ni in zama Darekta Janar. Mun zo nan ne domin fada masu abin da muke tsammani da abin da mu ke sa ran samu a matsayin jam’iyya.

Kara karanta wannan

'Ni na ci zaɓe a 2023': Kalaman Obi da suka dugunzuma fadar shugaban ƙasa

Sanata Yari yana neman agajin Zamfarawa

‘Dan majalisar yana fatan mutanen jihar Zamfara za su nuna wa Tinubu gagarumin goyon baya a zaben shugaaban kasa na 2027.

Ban da irin wannan zama da aka yi, akwai tuntubar jama’a da haduwa da masu ruwa da tsaki da gangami da Yari za su shirya.

Wajen gangamin ne za a rika fada wa 'yan Najeriya nasarorin da APC ta samu a matakin tarayya.

Meya hana Peter Obi ya bi Atiku Abubakar?

A nan aka ji labari Peter Obi ya ce bai ƙi tayin zama mataimakin Atiku ba kuma ya yi zancen yafe masa takara a zaɓe mai zuwa.

Ya ce jam’iyyun NDC da ADC ne kawai ke da alhaki da ikon yanke shawarar haɗa kai a tsakaninsu domin tsaya takara a tikiti guda.

Ttun farko Obi ya ce ba a zauna da shi aka yi masa tayin zama mataimakin shugaban ƙasa ba, amma yana mai buɗe kofa ga hadaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng