Tarihin Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris

Tarihin Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris

Yayin da ake ta bikin Mai martaba Sarki Shehu Idris na Zariya, Legit.ng Hausa ta tsakuro maku kadan daga cikin tarihin rayuwar wannan babban Sarki na kasar Arewa.

Alhaji Shehu Idris ‘Da ne wajen Idris Auta, wanda shi kuma ya na cikin ‘Ya ‘yan Sarki Malam Sambo. Silarsu ta tike da Malam Abdulkarimu wanda ya fara mulki a 1834.

.1. Tarihi ya tabbatar da cewa an haifi Alhaji Shehu Idris ne a shekarar 1936 a Garin Zariya.

2. Mahaifinsa Idris Auta ya mutu ne yayin da Mai martaba yak e da shekaru 12 rak a Duniya.

3. Kakansa shi ne Sarki Muhammad Sambo wanda ya shafe shekaru kusan goma ya na sarauta a Zariya.

4. Mai martaba yayi karatun addinin Musulunci hannun Malamai a lokacin da ya ke tasowa.

5. Shehu Idris ya halarci makarantar Middle ta Zariya. Dagan a ya tafi makarantar karantarwa ta Katsina.

6. Bayan ya kammala karatu a Katsina Training College, sai Mai martaba ya zama Malamin makaranta.

7. A shekarar 1960, Shehu Idris ya zama Magatakardan Sarki Muhammadu Aminu a cikin fada.

KU KARANTA: Sarauniyan kasar Iwo ta yi murabus bayan Sarki ya sake ta

8. A shekarar 1967, Alhaji Shehu Idris ya yi kwas a Makarantar koyar da aikin gwamnati da ke Zariya.

9. A shekarar 1973 ne aka nada Mai martaba a matsayin Hakimin Birnin Zariya da kewaye.

10. A wannan shekara ne kuma ya samu sarautar Dan Madamin Zazzau.

11. Jim kadan bayan nan sai Sarki Aminu ya rasu, inda Shehu Idris ya gaje sa a Fubrairun 1975.

12. Shehu Idris shi ne Sarki na 18 da na Fulani da aka yi a kasar Zazzau.

13. Sarkin Zazzau ya fito ne daga gidan Katsinawan da su ka yi mulki a kasar Zariya.

14. Mai martaba ya na da Mata hudu da tarin ‘Ya ‘ya masu albarka.

15. Alhaji Shehu Idris ya hau kan gadon mulki ya na shekara 39. Jiya ya shafe shekaru 45 ya na sarauta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng