An Fara Fito da Abubuwan da Tinubu Ya Shirya Yi a Najerirya idan Ya Lashe Zaben 2027
- Gwamna Chukwuma Soludo ya ce wa’adin mulki na biyu na Bola Tinubu zai samar da Najeriya mai ƙarfi da adalci
- Soludo ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar wahalhalu, amma ya ce har yanzu akwai fatan samun sauyi nagari
- Oluremi Tinubu ta tallafa wa mata 500 daga yankin Kudu maso Gabas, yayin da Nonye Soludo ta tallafa wa mata 5,000 a Anambra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra, Nigeria - Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya fara hasashen abubuwan da Shugaba Bola Tinubu zai yi wa Najeriya a wa'adin mulkinsa na biyu.
Soludo ya bayyana kyakkyawan fata cewa wa’adin mulki na biyu na Shugaba Bola Tinubu zai samar da “Najeriya mai ƙarfi da adalci”, duk da cewa akwai wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta a yanzu.

Source: Twitter
Leadership ta ce Soludo ya bayyana hakan ne a Awka yayin wata liyafar da aka shirya domin karrama Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a dandalin Alex Ekwueme Square.

Kara karanta wannan
2027: Sanata Yari ya yanke hukunci kan wanda ya cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi
Gwamna Soludo ya hango sauki
An kuma gudanar da bikin ne a matsayin ƙaddamar da shirin samar da abinci na Renewed Hope Initiative (RHI) na shiyyar Kudu maso Gabas.
Gwamnan ya ce:
“Ko da yake ina jin raɗaɗin waɗanda ke korafi a yanzu, ina ganin akwai haske. Har yanzu akwai alamun cutar kansa, amma akwai fata ta samun waraka. Shekaru huɗu na gaba na Tinubu za su samar da Najeriya mai ƙarfi da adalci.
Oluremi ta raba tallafi ga mata
A wani ɓangare na shirin tallafin RHI, Uwargida Oluremi Tinubu ta tallafa wa mata 500 da aka zaɓo daga sassa daban-daban na shiyyar Kudu maso Gabas.
A nata ɓangaren, matar Gwamnan Anambra, Dakta Nonye Soludo, ta tallafa wa mata 5,000 a jihar. Uwargidan Shugaban Ƙasa ta sanar da bayar da N100,000 ga kowace daga cikin waɗanda suka amfana.
Uwargida Tinubu ta ce Anambra tana da “wuri na musamman a zuciyata”, tana mai bayyana cewa tana da taken sarauta guda huɗu a ƙasar Igbo.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya
“Mun tallafa wa mata 500 jiya, yayin da a yau Anambra ta tallafa wa 5,000. Zan bai wa kowacce mai cin gajiyar tallafin N100,000. Muna matuƙar farin ciki da abin da muke gani.
“Ina kira da a kai dukkan iyaye mata masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki zuwa cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko a dukkan shiyyoyin ƙasa. Mutanen Igbo mutane ne masu kirki. Zan dawo domin yin kamfe.”
- Oluremi Tinubu.
Daga bisani, Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Anambra ta ba Uwargidan Shugaban Ƙasa taken sarauta na “Ugo Eze Anambra”, wato “Gaggafa ta Sarki”.
Shugaban majalisar, kuma Sarkin Obosi da ke Ƙaramar Hukumar Idemili North, Igwe Chidubem Iweka, ya ce an karrama Sanata Oluremi Tinubu ne saboda tausayi da hidimar da take yi wa ’yan Najeriya marasa galihu.
Dakta Nonye Soludo ta bayyana Bankin Abinci na RHI a matsayin “shaida bayyananniya ta kula da talakawa”, inda ta ƙara da cewa babu wata Uwargidan Shugaban Ƙasa da ta gabata da ta kula da rayuwar ’yan Najeriya marasa galihu kamar yadda Uwargida Tinubu ta yi.
Asali: Legit.ng