Abdulaziz Yari Ya Fadi Sirri da Ya Kama Aikin Tallar Tinubu babu Kama Hannun Yaro

Abdulaziz Yari Ya Fadi Sirri da Ya Kama Aikin Tallar Tinubu babu Kama Hannun Yaro

  • Abdulaziz Yari ya ce an kawo manufofi da nufin gyara tattalin arziki kuma a samu kudin shiga ne ba a matsawa talakawa ba
  • Ya ce Gwamnatin Tarayya ta kashe abin da ya fi dala miliyan 7 wajen sayen makamai don magance matsalar tsaro a Najeriya
  • Yari ya bayyana yadda Gwamnatin Bola Tinubu ta jawo lalitar gwamnonin jihohi suka cika saboda sauyin da aka yi a 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Zamfara - Abdulaziz Abubakar Yari ya tare a jihar Zamfara a matsayin shi na Darekta janar na kamfen shugaban kasa.

Shugaban yakin neman zaben na Bola Ahmed Tinubu ya ce za su yi amfani da dabaru dabam-dabam domin APC ta ci zabe.

Yari da Tinubu
Abdulaziz Yari da Bola Tinubu a ofishinsa a Abuja Hoto: @NaijaPR/Bayo Onanuga
Source: UGC

Abdulaziz Yari ya kare manufofin Bola Tinubu

A ranar Juma’a Daily Trust ta rahoto Abdulaziz Yari yana kare wasu matakai da ayyukan da Bola Tinubu ya yi a ofis.

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari ya fadi yadda ya zama sarkin yakin zaben Tinubu cikin dubunnan 'yan APC

Shi kan shi Yari ya yarda ana shan wahala a sanadiyyar manufofin da Bola Tinubu ya kawo da sunan gyaran tattalin arziki.

Amma ‘dan siyasar ya ce daukar wadannan matakai masu wahalarwa sun zama dole idan ana so a daura kasar a kan turba.

Abdulaziz Yari ya ce:

“Wasu manufofi ne masu ciwo da dole a dauka domin cigaban tattalin arziki.
“Muna aiki babu kakkautawa a Najeriya. Asiwaju yana aiki babu dare-babu rana, yana tunanin ya Najeriya za ta kasance.

Da aka yi zancen haraji, ya ce gwamnatin APC ta sauya tsare-tsaren haraji ta yadda mutane za su biya daidai da aljihunsu.

Yari ya ce ba a matsa wa talakawa lamba da harajin ba domin ana duba karfin aljihun kowa.

"Mun ce za mu tatsi harajinmu daidai da samu. Ba za mu tatsi talakawa ba, mu jawo su sha wahala a sabon tsarin harajin nan.

Kara karanta wannan

Matar Atiku ta shigo fage, Titi ta yi magana game da mulkin Shugaba Tinubu

"Wadanda ba su biya za su biya, wadanda suke samun kudi kuma za su biya daidai gwargwadon samunsu."

- Abdulaziz Yari

Idan aka yi amfani da tsarin da kyau, Sanata Yari ya ce gwamnatin Najeriya za ta samu kudin da zai iya rike tattalin arziki.

Tsohon gwamnan ya yi bayanin karin kudin da gwamnoni suka samu saboda kudin shiga, ya kamanta da lokacin mulkinsa.

Tinubu ya kashe $7bn a sayen makamai

Ta fannin tsaro, Darekta janar na kamfen din ya ce gwamnatin Tinubu tana kashe kudi masu yawa domin yaki da rashin tsaro.

A nan ne ya ce Tinubu ya nuna masa takardar da ta tabbatar da ya sayo makaman sama da $7m da ya karbi mulkin kasar nan

Da yake bayanin wannan sirri, Yari yace yana fatan gwamnatin Tinubu za ta kawo karshen ‘yan ta’addan da ake fama da su.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da Kashim Shettima da sauran musulmai a masallaci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

‘Zama DG aikin Allah ne’, Yari

Abdulaziz Yari ya yi bayanin yadda aka dauko shi ya jagoranci kamfen tazarcen Bola Tinubu da Kashim Shettima a APC.

Kara karanta wannan

'Abin da tsofaffin shugabanni ke tsoro Tinubu ya aiwatar saboda tausayin 'yan kasa'

An rahoto sanatan ya ce Allah ne ya zabe shi domin ya zama Darekta Janar na yakin zaben shugaban kasa a zaben 2027.

Tsohon gwamnan ya yanke shawarar fara yakin neman zaben daga mahaifarsa ta jihar Zamfara kafin ya je sauran sassan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng