'Wataƙila Malamansa Suka Hana Shi', Baba Ahmed kan Kashim da Ƙin Sa Hular Tinubu
- Yusuf Datti Baba-Ahmed ya jefi Kashim Shettima da aiki da malamai, yana daukar abin da suka fada masa
- Maganar ta jawo wani mataimaki a Aso Rock ya yi wa ‘dan takaran na mataimakin shugaban kasa a LP martani
- Dr. Yusuf Datti ya ce malamai suka fada wa Shettima ya guji sanya hular magoya baya Asiwaju a kan shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babban ‘dan adawa, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya sake jefo wasu maganganun da za su iya tada kurar gaske a Najeriya.
Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed ya zargi Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima da yin amfani da malamai na tsibbu.

Source: Facebook
Datti Baba-Ahmed ya saki maganganu wajen hira
A wata hira da aka yi da shi a shirin MicOn a Facebook, ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar a 2023, an kawo zancen Shettima.
Akwai wata hula mai tambarin Asiwaju wanda mabiya da magoya bayan shugaban kasar suka saba sa wa domin nuna mubaya’arsu.
Baba-Ahmed ya ce mataimakin na Tinubu bai amfani da hular, ya kuma alakanta batun da cewa kila ya bi shawarar malamansa ne.
Ya shaida wa Seun Okinbaloye cewa babu mamaki malaman Shettima ne suka gargade shi da ya guji sanya hular Tinubu a kansa.
“Ina tunani malamansa ne suka fada masa kada ya sanya ta. Duka jagrorin APC suna sa hular. Ku tambaye shi meyasa malamai suka ce kada ya sanya ta (hular).
- Yusuf Datti Baba-Ahmed
Kashim Shettima yana yin aiki da malamai?
Mista Seun Okinbaloye ya tambaye shi ko mataimakin shugaban kasar yana da malamai, sai ya amsa yana nuna ba zai rasa su ba.
Ya ce:
"Yana da malamai da suke yi masa addu’a. Shakka babu zan iya fadar wannan."
Yusuf Datti Baba-Ahmed yake cewa ana dauko malamai daga ketare su zo kasar nan yayin zabe
"Shettima zai iya cewa bai da malamai. To, su wane ne abokansa a kasashen nan?
"Me ka ke kawo su nan su yi? A ranar zabe kuma meyasa wasu suke bacewa”
Babu ruwan Datti Baba-Ahmed da malamai
Datti wanda mahaifinsa malami ne da ya zo Najeriya daga kasar Mauritaniya ya ce shi bai da wasu malaman da suke yi masa wasu addu’o'i.
“Ni ban da su. Ina yi wa kai na addu’a dai, iyali, abokai da dangi muna yin addu’a, irin wanda mu ke yi kenan.
"Ba za ka taba samun wani can yana kiran kan shi malami ko wani mai tsibbu na ba."
- in ji 'dan siyasar
Tsohon ‘dan takaran na LP ya ce idan aka kai shi bango, zai fito da wasu bayanai domin ya san surkulen da ake yi lokacin yakin neman zabe.
Ya ce shi dai bai tura wa a dauko malamai daga kasashen Afrika saboda burin siyasa kuma bai tura mutane iyakar Najeriya ranar zabe.
Hadimi a Aso Rock ya wanke Shettima
Saboda haka Mahmud Muhammad ya yi masa raddi a shafin Facebook ranar Litinin, ya yi kaca-kaca da shi kuma ya karyata ikirarin shi.
Kwamred Mahmud Muhammad wanda hadimi ne a fadar shugaban kasa ya wallafa hotunan Shettima rututu yana dauke da hular Tinubu.
Ya yi tir da wannan salon adawa kuma yana mai kira a yi Allah-wadai da irin wannan siyasa ta ‘dan adawar da APC ta doke su a 2023.
Bidiyon bagaren hirar da shafin Heart to Heart with Sammy ya wallafa a sahar Facebook.
Yadda Shettima ya yi bikin cika shekara 60
An ji labari Kashim Shettima ya bukaci abokai da masoya da kada su kashe kudi wajen tallar taya shi murna ko shirya bikin cikarsa shekaru 60.
Maimakon kashe kudi wajen bukukuwa da kyaututtuka, ya roki masoyansa da su yi amfani da kudaden wajen ba da sadaka ga mabakata a Najeriya.
Haka zalika, ya nemi 'yan Najeriya da su mayar da hankali wajen yi wa kasar addu'o'in samun nasara, zaman lafiya da kuma ci gaba a lokacin.
Asali: Legit.ng


