Yaki Ya Yi Tsanani: Trump Ya Fadi Lokacin da Rigimarsa da Iran Za Ta Zo Karshe

Yaki Ya Yi Tsanani: Trump Ya Fadi Lokacin da Rigimarsa da Iran Za Ta Zo Karshe

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi imanin yakin da Iran zai kawo karshe bayan zaben tsakiyar wa’adin Amurka a watan Nuwamba
  • Trump ya yi zargin cewa Iran na kokarin tsawaita yakin domin rikita zaben, amma ya ce Amurkawa sun fahimci abin da ke faruwa
  • Ya ce farashin man fetur zai fadi matuka bayan kawo karshen yakin, yayin da yake magana da manema labarai a Dublin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana mai kama hankali game da yakin kasarsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya yi imanin cewa yakin da Iran zai kawo karshe bayan kammala zaben tsakiyar wa’adin Amurka da za a gudanar a watan Nuwambar shekarar 2026 mai zuwa

Trump ya magantu kan yakin Amurka da Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Dublin, inda ya ce kawo karshen yakin zai haifar da gagarumin saukar farashin man fetur, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Wasu matasa da aka sa a kwamitin yakin zabe sun wulakanta Tinubu a gaban kowa

Trump ya shiga layin da na nashi ba

Wannan na zuwa ne bayan Donald Trump ya yi katobara inda ya shiga hurumin Ubangiji madaukakin Sarki game da rayuwar wasu.

Donald Trump ya gargadi magoya bayansa na jam’iyyar Republican cewa za su “je wutar jahannama” idan ba su fito sun yi zaɓe a watan Nuwamba ba.

Shugaban Amurkan ya bukaci magoya bayansa su tattaro ’yan uwa da abokai domin kada su bari jam’iyyar Democrat ta samu nasara.

Trump ya ce nasarar Democrat a zaɓen Nuwamba za ta iya dawo da hannun agogo baya baya kan nasarorin gwamnatinsa wanda ya ke ganin hakan ba karamar barazana ba ce.

Abin da Trump ya ce game da Iran
Jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Trump ya magantu kan Iran game da yaki

Trump ya bayyana cewa Iran na kokarin ci gaba da yakin na tsawon lokacin da zai iya domin kawo cikas ga zaben, amma ya yi imanin jama’a sun fahimci manufar.

Shugaban ya bayyana tasirin da zaben zai yi game da yakin da ake ci gaba da yi tsakanin Amurka da Iran na tsawon watanni da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi, kamar yadda Anadolu Ajansi ta ce.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai ragargaji Atiku da Tinubu a zaben 2027 a Kano

Trump ya ce:

“Ina ganin nan ba da jimawa ba. Ina ganin mai yiwuwa hakan zai kasance nan da nan bayan zaben tsakiyar wa’adin. Suna kokarin jurewa gwargwadon yadda za su iya domin rikita zaben. Amma ina ganin mutane sun fahimci abin da suke yi.
“Idan hakan ya faru, farashin man fetur zai fadi matuka.”

Trump ya ki amincewa da rokon Saudiyya

A wani labarin, an ji cewa Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman ya kira Shugaba Trump sau biyu yana neman Amurka ta kai hare-hare kan mayakan Houthi.

Trump ya ƙi amincewa da buƙatar, yayin da jami’an Amurka suka ce gwamnatin Amurka ba ta shirin shiga yaƙi kai tsaye da Houthi a yanzu.

Ƙwace wani muhimmin birnin gabar tekun Yemen da Houthis suka yi ya sa farashin man fetur ya tashi saboda barazanar mashigar Bab al-Mandab.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.