Aliko Dangote Ya Yi Bayanin Abin da Ya Sa Zai Saida Hannun Jari a matatarsa

Aliko Dangote Ya Yi Bayanin Abin da Ya Sa Zai Saida Hannun Jari a matatarsa

  • Manufar sayar da hannun jarin da za su yi ita ce ba kowa damar mallakar kaso a Dangote maimakon neman kudi kawai
  • Masu zuba jari za su iya farawa da sayen karancin hannun jari guda 10, matatar za ta saida hannun jari har miliyan 10
  • Aliko Dangote yana fatan wannan jari zai zama mai dorewa kuma mai sauya rayuwar al'umma bayan tsawon shekaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Aliko Dangote ya ce suna harin saida hannun jari miliyan 10 a Afrika da suka sa matatar mai da ke Legas a kasuwa.

Aliko Dangote wanda shi ne mai kudin nahiyar Afrika ya ce za su saida hannun jari ne saboda a fadada mallakar matatar.

Dangote
Aliko Dangote da diyarsa wajen bikin sa hannu a IPO Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Meyasa Dangote suka sa hannun jari a kasuwa?

A makon nan aka rahoto Alhaji Aliko Dangote a tashar Arise yana magana game da hannun jarin da za su saida a Satumba.

Kara karanta wannan

Dangote ya tabo batun hannun jari, ya faɗi yadda ƴan Najeriya za su yi arziki

‘Dan kasuwar ya yi wannan zance ne a wani taro a Legas wajen bikin sa hannun sa hannun jarin matatar mansa a kasuwa.

Dangote ya ce ba kudi yake nema ba, illa dai ya ga ‘yan Afrika sun shigo cikin harkar kasuwancinsa domin su ma a dama da su.

A cewarsa, kamfaninsa yana samun kudi sosai a halin yanzu, amma za a sa jarinsa a kasuwa ne saboda a shigo da jama’a.

Alhaji Dangote ya ce da kudi kurum ake nema, da za a zabi masu zuba hannun jari sosai ne, amma sai suka tsuke lamarin.

“Idan kudi muke son tarawa, mun san yadda za mu nema. Shiyasa mu ke da iyaka. Idan da ba haka, da 20% na kamfanin za mu sa.”

- Aliko Dangote

Ana fata Dangote ya bi sahun Amazon & Coke

A wani bidiyo da The Cable ta daura a X, an ji shi yana misali da kamfanonin Amazon da Coke da suka saida hannun jarinsu a baya.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito: An ji abubuwan da suka faru da Ɗan Shagamu kafin a kashe shi a Kano

Dangote ya ce:

“Ina so ya zama irinsu Amazon da Coke, inda mutum zai saye hannun jarin $10, 000. Bayan ‘yan shekaru darajarsa sai ta kai miliyoyi.”

Babban mai kudin ya bayyana yadda Dangote yake fadada kasuwancinsa, baya ga mai sun shiga harkar hada takin zamani da kyau.

“Ba mu so a ce mu kadai mu ke jin dadi. Saboda haka mu ka baza wannan jin dadi zuwa sauran wurare a Afrika.”

- In ji shi

Ana sa ran a dade ana cin moriyar wannan matatar mai domin kuwa ba ta shekara 10, 20, 30 ko 50, yanzu ma ta fara aiki gadan-gadan.

Dangote
Aliko Dangote a wajen bikin sa hannun shirya saida hannun jari a matara mai Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wuraren da mutum zai iya sayen hannun jarin Dangote

An ji labari matatar Dangote ta amince da hanyoyi 32 da suka ƙunshi bankuna, kamfanonin fasahar kuɗi da kamfanonin sadarwa don sayen hannun jari.

Matatar ta yi gargadin cewa masu zuba jari su yi amfani da waɗannan sahihan kafofi ne kaɗai domin kiyaye kudinsu daga fadawa hannun 'yan damfara.

Domin sayen hannun jarin, masu buƙata na aiki da dillalan hannayen jari masu lasisi daga SEC da NGX sannan a haɗa shi da asusunsu na CSCS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng