Sarkin Ya Ji Dadin Kokarin Uba Sani, Ya Fadi Wahalar da Sarakuna Ke Ciki
- Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli, ya goyi bayan karin albashin sarakunan gargajiya da aka shirya a Kaduna
- Bamalli ya ce karin zai taimaka wa masarautun gargajiya, yayin da ya bayyana cewa Zazzau ta warware fiye da shari’o’in farar hula 2,000
- Sarkin ya ce masarautar Zazzau na hada kai da gwamnati da jami’an tsaro, tare da bayar da rahotannin sirri domin zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Sarkin Zazzau kuma shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Kaduna, Ambasada Ahmed Bamalli, ya yaba wa Gwamna Uba Sani na Kaduna.
Basaraen ya goyi bayan shirin kara albashi da alawus din sarakunan gargajiya da kashi 100 da gwamnatin Kaduna ta shirya.

Source: Facebook
Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa da ke Zariya, Kaduna, cewar Punch.
Sarkin Zazzau ya yaba wa Uba Sani
Bamalli ya bayyana karin a matsayin “sauki mai matukar amfani” ga masarautun gargajiya, yana cewa albashin da suke karba yanzu bai wadatar ba saboda tsadar rayuwa da faduwar darajar naira.
Ya bayyana cewa shirin karin albashin ya kwashe kusan watanni bakwai ana shirya shi, yana mai cewa Gwamna Uba Sani da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Sadiq Mamman-Lagos, suna aiki domin tabbatar da aiwatar da shi.
Bamalli ya ce bayan sanarwar da gwamnati ta fitar a hukumance, yana da yakinin cewa sabon tsarin albashin zai zama gaskiya nan ba da jimawa ba.
Ya ce:
“Karin da aka gabatar sauki ne mai matukar amfani ga masarautun gargajiya. Darajar kudi ta ragu sosai, kuma abin da sarakunan gargajiya ke karba yanzu bai isa ba idan aka kwatanta da wasu masarautu.”

Source: UGC
Alakar da ke tsakanin sarakuna da gwamnati
Sarkin ya yabawa Gwamna Sani da Mamman-Lagos saboda abin da ya bayyana a matsayin kulawa, kauna da jajircewarsu wajen tallafa wa masarautun gargajiya na jihar.
Ya ce kyakkyawar alakar da ke tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya ta taimaka wajen samar da shawarwari da hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafi al’umma.
A cewar Sarki Bamalli, sarakunan gargajiya ba ‘yan siyasa ba ne, amma suna taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da gwamnati, musamman wajen warware rikice-rikice da zaman lafiya.
Ya bayyana cewa Masarautar Zazzau ta warware fiye da shari’o’in farar hula 2,000 ta hanyar tsarin sasanta rikice-rikice ba tare da zuwa kotu ba cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya ce wannan tsari ya taimaka wajen rage cunkoso da matsin lamba kan kotunan yau da kullum, inda fadar ke karbar matsakaitan shari’o’i biyar a kullum daga Litinin zuwa Alhamis.
Sarkin Zazzau ya ba magidanta shawara
Mun ba ku labarin cewa Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli ya yi magana kan halin tsadar rayuwa da ake fama da shi a ƙasar nan.
Mai martaba sarkin ya buƙaci magidanta masu ƙaramin ƙarfi da ka da su auri mace fiye da ɗaya domin su samu damar sauke nauyin da ke kansu.
Ya koka da yadda mutane suke tara ƴaƴa masu yawa duk da ba su da sukuni ko wadatar da za su iya kula da su yadda ya dace.
Asali: Legit.ng

