Atiku Ya ba da Mamaki, Ya Yi Godiya ga Wata Mata da Ta Masa Ruwan Addu'o'i

Atiku Ya ba da Mamaki, Ya Yi Godiya ga Wata Mata da Ta Masa Ruwan Addu'o'i

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya amsa addu’ar wata mata mai suna Khadijat da ta roƙi Allah Ya sauƙaƙa masa cika alkawuran da ya yi
  • Atiku ya gode mata tare da bayyana yadda tsarin tallafin samar da man fetur da yake gabatarwa zai iya rage wa iyalan Najeriya nauyin rayuwa
  • Ya ce manufar shirin ita ce tallafa wa man da ake tacewa a Najeriya, samar da ayyukan yi da rage kuɗin fetur domin rayuwar jama'a ta samu sauƙi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya amsa addu’ar wata mata mai suna Khadijat, wadda ta roƙi Allah Ya sauƙaƙa masa cika alkawuran da ya yi.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da caccaka tsinke kan batun maido tallafin man fetur bayan zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

Hankalin Dangote ya tashi kan maido tallafin mai, Atiku ya masa bayani dalla dalla

Atiku Abubakar da matar da ta masa addu'a
Atiku Abubakar a hagu, Khadijat a dama. Hoto: @khadyashdee|@Atiku
Source: Twitter

Matar ta rubuta addu’ar ne a shafinta na X bayan Atiku ya yi karin bayani kan shirin tallafin samar da man fetur da ya gabatar.

Atiku ya gode wa Khadijat

A sakon da matar mai suna Khadijat ta wallafa ta roki Allah ya ba Atiku Abubakar damar sauke nauyin da ya dauka idan ya ci zaben 2027.

“Allah Ya sauƙaƙa maka cika dukkan waɗannan alkawura. Amin Ya Rabb.”

Da yake mayar da martani, Atiku ya ce:

“Amin Ya Rabbi, Khadijat. Allah Ya saka miki da alheri saboda kyakkyawar addu’arki. Allah Ya karɓe ta, Ya saka miki da alheri mai yawa.”

Ya kuma roƙe ta da ta taimaka wajen bayyana wa wasu mata da makusantanta manufar shirin nasa.

Ya ce:

“Ki taimaka ki bayyana wannan shiri ga abokanki, ’yan uwanki mata da maƙwabtanki.”

Tsarin tallafin mai na Atiku

Atiku ya ce ya kamata mutane su yi tunanin halin matar da take tashi da sassafe, ta shirya ’ya’yanta zuwa makaranta, ta je kasuwa, ta ci gaba da tafiyar da ƙaramin sana’arta sannan ta tabbatar da cewa akwai abinci a gida da dare.

Kara karanta wannan

"A wasu lokutan," Ana zargin ba Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulkin Najeriya ba

Ya ce idan farashin man fetur ya ragu, kuɗin sufuri zai ragu, abin da take saya a kasuwa na iya raguwa, sannan gudanar da sana’arta zai zama mafi sauƙi.

Atiku Abubakar da abokin takarar shi
Rotimi Amaechi da Atiku Abubakar. Hoto: Paul O Ibe.
Source: Facebook

A martanin da ya yi a X, Atiku ya ce hakan zai ba ta damar samun ƙarin kuɗin da za ta iya amfani da shi wajen kula da ’ya’yanta da gidanta.

Atiku ya ce:

“Irin wannan sauƙi ne nake son matan Najeriya su ji a rayuwarsu ta yau da kullum.”

Martanin Atiku ga Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya ce damuwar da Matatar Dangote ta nuna kan tilasta wa matatun mai sayar da fetur a farashin da ba ya kawo riba ta ƙarfafa matsayarsa ta tallafin samar da man fetur.

Atiku ya ce gargaɗin Dangote cewa bai kamata a tilasta wa matatun mai masu zaman kansu sayar da fetur cikin asara ba, abin dubawa ne a harkar kasuwanci.

Ya ce shirin nasa ba zai tilasta wa matatun cikin gida sayar da man fetur a ƙasa da kuɗin samarwa ba, sai dai zai rage kuɗin ɗanyen man da ake bai wa matatun Najeriya da suka cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng