Bayan Korafi kan Tallafi, Dangote Ya Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

Bayan Korafi kan Tallafi, Dangote Ya Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

  • Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur da take sayarwa a farfajiyar matatar da Na85 kan kowace lita, daga N1,265 zuwa N1,350
  • Ƙarin ya zo ne yayin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuɗin maye gurbin man fetur ke ci gaba da tashi
  • Sabon farashin ya haura matsakaicin kuɗin saukar da man fetur na yanzu da aka sanya a N1,311 kan lita, abin da ke ƙara matsin lamba a harkar mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur da N85 kan kowace lita, inda farashin da take sayar wa dillalai ya tashi daga N1,265 zuwa N1,350.

Ƙarin farashin da aka ruwaito ya kai kashi 6.7 cikin 100, yayin da farashin ɗanyen mai da kuɗin maye gurbin man fetur a kasuwannin duniya ke ƙaruwa.

Kara karanta wannan

Houthi sun kwace yankin Bab al Mandab yayin da Saudi ke naman agajin Trump

Aliko Dangote da matatar shi
Alhaji Aliko Dangote a hagu, matatar shi a dama. Hoto: Dangote Industries|Getty Images
Source: Facebook

Dangote ta ƙara farashin mai

The Sun ta wallafa cewa sabon farashin Matatar Dangote ya haura matsakaicin kuɗin saukar da man fetur na yanzu wanda aka kiyasta a N1,311 kan kowace lita.

Wannan na ƙara rikita harkokin farashi ga masu ajiyar man fetur da dillalan da ke dogaro da sayen man daga matatun cikin gida.

Matatar ta daɗe tana sayar da man fetur a farashin N1,265 kan lita a Legas duk da hauhawar farashin mai a kasuwannin duniya.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa ƙarin farashin ɗanyen mai da kuɗin maye gurbin man fetur ya sa aka sake duba farashin.

Dillalai sun fara sauya farashi

Tasirin sabon farashin ya fara bayyana a kasuwar man fetur, inda wasu masu ajiyar mai ke sauya farashinsu da adadin man da suke ajiyewa saboda fargabar ƙarin kuɗin maye gurbin man.

Masu harkar man fetur sun ce matsin lambar ya wuce Legas, inda ake samun irin wannan yanayi a manyan cibiyoyin kasuwancin man fetur na gabar teku kamar Warri, Fatakwal da Calabar.

Kara karanta wannan

Karin kudin fetur babu makawa yayin da ake wayyo lita ta haura N1300

Mutane na sayen mai
Yadda ake sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai farashin da dillalai ke sayar da man a rumbun ajiya ya bambanta daga mai sayarwa zuwa wani, inda ake sa ran hakan zai bayyana a gidajen mai.

Rahoton Business Day ya nuna cewa hakan na da alaƙa da yawan man da suke da shi, inda suka samo shi da kuma yanayin kasuwa a lokacin.

Martanin Atiku ga Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya goyi bayan gargaɗin Matatar Dangote kan tilasta wa matatun mai sayar da man fetur a farashin da zai jefa su cikin asara.

Atiku ya ce tsarin tallafin samar da mai da ya gabatar zai taimaka wajen rage kuɗin samar da man fetur a matatun cikin Najeriya ba tare da tilasta musu sayarwa cikin asara ba.

Ya bayyana cewa shawararsa ta bambanta da tallafin shigo da man fetur, domin tsarin nasa zai tallafa wa ɗanyen mai da ake tacewa a Najeriya domin rage kuɗin samar da man fetur ga ’yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng