Gargadin Ƴan Sanda ga Al'ummar Sokoto bayan Hari kan Sheikh Lukuwa a Masallaci

Gargadin Ƴan Sanda ga Al'ummar Sokoto bayan Hari kan Sheikh Lukuwa a Masallaci

  • Yan sanda a jihar Sokoto sun yi magana game da harin da aka kai wa Sheikh Musa Lukuwa a bayan idan da sallar Juma'a
  • Musa Lukawa ya tsira daga harin da aka kai masa a Masallacin Lukuwa bayan sallar Juma’a, inda aka yi masa rauni a wuya da hannun hagu
  • ‘Yan sanda sun ce fusatattun mutane sun kashe wanda ake zargin bayan sun cafke shi jim kadan bayan harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Rundunar ‘Yan Sandan Sokoto ta ja hankalin al'ummar jihar bayan mummunan hari kan Sheikh Musa Lukuwa.

Yan sanda sun yi kira ga jama’a su kwantar da hankula tare da guje wa ɗaukar fansa bayan harin da aka kai.

Yan sanda sun yi magana kan farmakin Lukuwa
Kwamishinan yan sanda a Sokoto, Hayatu Hassan da Sheikh Musa Lukuwa. Hoto: Sokoto Police Command, Murtala Bello Sokoto.
Source: Facebook

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Ahmad Rufai, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Juma’a, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Malam Murtala Bello ya faɗi shirinsu da aka kai wa Sheikh Lukuwa hari a Sokoto

Yadda aka farmaki Sheikh Lukuwa a masallaci

Rundunar ta ce Lukawa ya tsira daga harin kuma an sallame shi daga asibiti bayan an yi masa magani kan raunukan da ya samu a wuya da hannun hagu.

An bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:50 na rana bayan rundunar ta samu kiran neman agaji daga wani ɗan kasa.

A cewarsa, wani mutum da ba a bayyana ko wanene ba ya shiga masallacin sannan ya kai wa malamin hari jim kaɗan bayan an kammala sallar Juma’a.

Ya ce daga bisani wasu fusatattun mutane sun cafke wanda ake zargin tare da kashe shi kafin jami’an tsaro su isa wurin.

Sanarwar ta ce:

“Maharin, wanda ya fito da wata wuƙa mai kaifi, ya yi wa wanda abin ya shafa mummunan yanka a wuya da hannun hagu.

Kara karanta wannan

Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna

"An garzaya da gawar maharin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa sannan aka ajiye gawarsa a dakin adana gawarwaki na UDUTH."
An farmaki Sheikh Lukuwa a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan sun yi Allah-wadai da farmakin Lukuwa

‘Yan sandan sun yi Allah-wadai da kashe wanda ake zargin, suna bayyana lamarin a matsayin ɗaukar doka a hannu, duk da fushin da harin da aka kai wa malamin ya jawo.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, ya bukaci jama’a su bari binciken ‘yan sanda ya gano abubuwan da suka haddasa lamarin.

“Yana da matuƙar muhimmanci mu bar doka ta yi aikinta domin tabbatar da an yi adalci yadda ya kamata."

- in ji kwamishinan.

Rundunar ta ce an tura jami’an tsaro yankin domin tabbatar da zaman lafiya da doka, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.

Ta kuma bukaci jama’a su kasance masu taka-tsantsan tare da kai rahoton abubuwan da suke zargi ga hukumomin tsaro, maimakon ɗaukar doka a hannunsu.

Abin da Sheikh Lukuwa ya ce bayan harin

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Musa Lukuwa ya yi martani bayan kai masa hari jim kaɗan bayan kammala sallar Juma'a a Sokoto.

Kara karanta wannan

An dauki mummunan mataki kan malamin addini bisa zargin batanci ga iyayen manzon Allah

Malamin ya ba masoya hakuri tare da yi masu albishir cewa babu abin da ke damunsa a yanzu inda ya yi godiya na musamman ga al'umma da suka nuna masa goyon baya.

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafofin sadarawa da yammacin yau Juma'a 11 ga watan Satumbar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.