Tashin Hankali: An Shiga cikin Gida An Kashe Babban Malamin Najeriya a Kasar Waje

Tashin Hankali: An Shiga cikin Gida An Kashe Babban Malamin Najeriya a Kasar Waje

  • Kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu (NICASA) ta tabbatar da kashe babban malamin coci, Fasto Taiwo Michael Fakunle a Johannesburg
  • An yi zargin cewa wasu mutane biyu sun shiga gidansa tare da harbe malamin wanda dan asalin Najeriya
  • NICASA ta buƙaci ’yan sandan Afirka ta Kudu su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda suka aikata kisan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Johannesburg - Kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu (NICASA) ta yi zargin cewa an kashe wani limamin coci dan Najeriya mai shekaru 58, Bishop Taiwo Michael Fakunle, a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu.

An yi zargin kashe FastonFakunle, ɗan asalin Iye da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti, ne ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba, 2026, a gidansa da ke Kensington, Johannesburg.

Kara karanta wannan

Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna

Bishop Taiwo Michael Fakunle
Limamim coci da aka kashe a kasar Afirka ta Kudu, Bishop Taiwo Michael Fakunle Hoto: Matthew Omeh
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban NICASA na ƙasa, Rabaran Frank Onyekwelu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis da ta wuce.

Yadda aka kashe faston Najeriya

Ya ce yanayin da ke tattare da mutuwar limamin ya jefa iyalansa, abokansa da ’yan Najeriya da ke ƙasar cikin babban alhini.

A cewarsa, wasu mutane biyu da ake zargi sun samu shiga gidan Fasto Fakunle sannan suka buɗe masa wuta, inda rahotanni suka ce sun harbe shi fiye da sau bakwai.

Onyekwelu ya bayyana lamarin a matsayin “mummunan tashin hankali”, yana mai yin Allah wadai da kisan tare da nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da rasa rayukan ’yan Najeriya a Afirka ta Kudu.

“Wannan ba kawai rasa rai na yau da kullum ba ne; mummunan tashin hankali ne marar ma’ana da ya ƙwace wa iyali wanda duke ƙauna, tare da ƙwace wa al’ummar Najeriya wata rayuwa mai daraja,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya saki bama bamai a Zamfara, an kashe Kachalla Gurgu

An fara bincike kan kisan malamin

Onyekwelu ya ce NICASA ta kai rahoton lamarin ga Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Johannesburg, sannan aka buɗe shari’ar kisan kai a Ofishin ’Yan Sanda na Jeppe.

Ya buƙaci Hukumar ’Yan Sandan Afirka ta Kudu (SAPS) da sauran hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike na gaskiya da gaskiya domin gano abin da ya faru da kuma dalilan da suka jawo kisan.

“Muna buƙatar cikakken bincike mai inganci wanda zai tabbatar da ainihin abin da ya faru, gano duk waɗanda ke da hannu, kama waɗanda suka aikata laifin tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci gwargwadon ƙarfin doka,” in ji shi.

NICASA ta kuma buƙaci hukumomin diflomasiyyar Najeriya da ke Afirka ta Kudu su ci gaba da tuntuɓar hukumomin ƙasar da abin ya shaa tare da bibiyar yadda binciken ke gudana har sai an tabbatar da an yi adalci.

Kara karanta wannan

Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu

Tinubu ya yi magana kan Afirka ta Kudu

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kasashen Afirka su hada murya wajen Allah wadai da hare-haren kyamar baki da ake kai wa baki a kasar Afirka ta Kudu.

Tinubu ya ce Najeriya ta kwashe sama da ’yan kasa 1,490 daga Afirka ta Kudu, tare da shirye-shiryen daukar karin matakai idan bukata ta taso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262