Sheikh Aminu Daurawa Ya Jero Matakan Tarbiyya da za Su Hana 'Ya'ya Lalacewa

Sheikh Aminu Daurawa Ya Jero Matakan Tarbiyya da za Su Hana 'Ya'ya Lalacewa

  • Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci iyaye su tarbiyyantar da ’ya’yansu cikin ƙauna, haƙuri da kyakkyawar magana domin su taso da kyawawan halaye
  • Ya ce ya kamata iyaye su koya wa yara girmama manya, tsafta, nutsuwa, zaɓar abokai nagari da kuma amfani da lokacinsu yadda ya dace
  • Sheikh Daurawa ya jaddada cewa ƙauna ita ce tushen tarbiyya, yana mai kira ga iyaye su saurari ’ya’yansu, su fahimce su kuma gyara kurakurensu cikin hikima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar KanoSheikh Aminu Daurawa ya bayyana wasu hanyoyin da iyaye za su bi wajen tarbiyyantar da ’ya’yansu cikin ƙauna da tausayi, domin su zama ’ya’ya nagari masu amfani ga kansu da al’umma.

Ya ce yaro yana koyon abubuwa da dama daga abin da yake gani da kuma abin da yake ji daga iyayensa, don haka ya kamata iyaye su zama abin koyi nagari a gare su.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 12 da aka taba samu da yi wa ‘yan adawa barazana lokacin zabe

Sheijh Aminu Ibrahim Daurawa
Malamin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Matakan tarbiyyar 'ya'ya

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Sheikh Daurawa ya bayyana wasu matakai da ya kamata iyaye su dauka domin yi wa 'ya'yansu tarbiyya..

karkashin koyar da halaye masu kyau, malamin ya ce:

1. Mu koya musu yawan gaishe da manya da girmama waɗanda suka fi su girma.

2. Mu koya masu nutsuwa, musamman lokacin da suke waje ko a hanya.

3. Mu koya masu tsafta da kyakkyawar shiga, cikin sauƙi da ladabi.

A bangaren taimakon yara su nisanci munanan halaye, Sheikh Daurawa ya ce:

1. Mu koya masu muhimmancin zama a gida da yawan amfani da lokacinsu yadda ya dace.

2. Mu taimaka masu wajen zaɓar abokai nagari, domin aboki yana da tasiri a tarbiyyar yaro.

3. Idan sun yi faɗa ko rashin kunya, mu gyara su cikin natsuwa, ba tare da wulaƙanta su ba.

Batun yi wa yara gyara

A bayanin da ya yi, Sheikh Daurawa ya bayyana muhimmancin yi wa yara gyara, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaban da ya nemi mata su kashe aurensu kan zaben APC ya magantu

1. Idan sun sa baki a maganar manya, mu koya masu lokacin da ya dace su yi magana.

2. Idan suka kawo tsegumi ko gulma, mu bayyana masu illarsa cikin tausayi.

3. Idan suka yi zagi ko suka karyata manya, mu nuna musu yadda ake magana cikin ladabi.

Game da koyawa yara addini kuma, malamin ya ce:

1. Mu koya masu muhimmancin Sallah tun suna ƙanana, cikin haƙuri da kyakkyawar hanya.

2. Mu koya masu cewa roƙo da kwaɗayi ba kyawawan halaye ba ne, tare da nuna musu godiya da wadatar zuci.

3. Idan suka yi ƙarya ko suka zama ragwaye, mu gyara su cikin hikima, mu nuna masu muhimmancin gaskiya da ƙoƙari.

A kan matakan jan yara a jiki, Malam Aminu Daurawa ya ce:

1. Idan sun balaga, mu ƙara kusantar su domin su samu damar tattaunawa da mu.

2. Idan ba su da lafiya, mu nuna masu kulawa da tausayi.

3. Idan muna gida tare, mu ba su lokaci, mu saurare su, mu fahimci abin da ke cikin zukatansu.

Kara karanta wannan

Christopher Musa ya yi wa Kwankwaso da Obi raddi, ya ce Tinubu zai zarce

A kan kwadaitar da yara su yi aiki mai kyau, Daurawa ya ce:

1. Mu ƙarfafa su kan karatu da rubutu.

2. Mu koya masu dagewa da haƙuri wajen cimma burinsu.

3. Mu tuna masu cewa nasara ta gaskiya tana zuwa ne tare da ƙoƙari, addu’a da bin hanyar Allah.

Bukatar koya masu abubuwa masu muhimmanci:

1. Riko da addinin Musulunci da kyawawan halaye.

2. Zumunci da ziyartar ‘yan uwa da dangi.

3. Muhimmancin lafiya, lokaci da damar ƙuruciya.

A kan kare su daga ayyukan da ba su dace ba, ya ce:

1. Mu guji tattauna sirrin aure ko wasu abubuwan manya a gabansu.

2. Mu kula da irin abubuwan da muke kalla ko wasa a gabansu.

3. Mu guji nuna masu rikicin aure ko rashin jituwa a tsakaninsu, domin hakan na iya shafar zukatansu.

Ya kara da cewa dole ne iyaye su zama abin koyi a gare su:

1. Mu yawaita karatun Alƙur’ani da salloli.

2. Mu nuna masu gaskiya da riƙon amana ta hanyar ayyukanmu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Abin da zai faru da masu zagi da sukar gwamnatin Tinubu

3. Mu yawaita godiyar Allah da wadatar zuci, domin su koya daga gare mu.

A game da daura yara a ka rashin tsoro maras amfani kuma, ya ce:

1. Mu koya musu cewa mutuwa gaskiya ce, amma kada mu sanya masu tsoro fiye da kima.

2. Mu koya musu cewa arziki daga Allah yake, tare da ƙarfafa su su yi aiki da ƙoƙari.

3. Mu koya musu kada su ji tsoron mutane fiye da yadda suke tsoron Allah.

Sheikh Aminu Daurawa
Sheikh Aminu Daurawa a wajen karatu. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Ya kara da cewa yana da kyau iyaye su goyi bayan 'ya'yansu idan suna da gaskiya:

1. Idan suna kan gaskiya, mu tsaya tare da su.

2. Idan ba su yi laifi ba, mu kare su cikin adalci.

3. Idan sun yi abin da ya dace domin kare mutuncinsu ko na iyalinsu, mu fahimce su kuma mu ba su shawara cikin hikima.

Ya bukaci a koyar da su illolin:

1. Haɗama da son abin da ba nasu ba.

2. Rigima da husuma.

3. Taƙama da girman kai.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga shirye shiryen dinke barakar da ta bijiro wa jam’iyyar a jihohi

Ya ce yana a kyau iyaye su rika tattaunawa da 'ya'yansu:

1. Mu sanar da su asalinsu da tarihin iyalinsu.

2. Mu koya masu game da mutuwa da kabari cikin hikima da fata ga rahamar Allah.

3. Mu bayyana masu cewa duniya ba ta dawwama, don su koyi amfani da rayuwarsu wajen aikata alheri.

A karshe, ya bukaci a koya masu yin abubuwa bisa daidai:

1. Mu koya masu kada su yi almubazzaranci wajen cin abinci.

2. Mu koya masu daidaita barci, hira da sauran abubuwan nishaɗi.

3. Mu ƙarfafa su su yi buri mai kyau, amma mu koya masu cewa nasara tana buƙatar aiki, haƙuri da tawakkali.

Legit ta tattauna da Aisha

Wata mahaifiya mai suna Aisha Muhammad ta bayyana cewa matakan da malamin ya jero za su yi matukar taimakawa.

Sai dai ta kara da cewa:

"Yana da muhimmanci mutane su dauki wannan bayani da muhimanci domin hakan zai taimaka masu sosai.
'Ba ko yaushe ake ba yara tarihin zuriyarsu ba, wannan babban kuskure ne gaskiya. Yana da kyau a mayar da hankali a kan hakan."

Kara karanta wannan

Bashin biliyoyi ya taru a kan Kiyosaki da ke koya wa mutane dabarun yin kudi

An jefar da jarirai a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa ’yan sandan Abuja sun ceto wasu jarirai biyu da aka yi watsi da su a wasu wurare daban-daban a Kurudu da Gwagwalada.

Kakakin rundunar ’yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta ce wani mazaunin Kurudu mai suna Innocent ya gano wani jariri yana kuka a ranar 2 ga Satumba, 2026.

Ta ce jami’an ’yan sanda tare da sashen JWC sun ceto jaririn, inda aka kai shi asibiti domin duba lafiyarsa, sannan aka mika shi ga sashen kula da jin daɗin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng