Muhimman Abubuwa 7 da Najeriya Ta Nema a Taron UNGA Karo na 81
- Najeriya ta nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin biyu a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya tare da cikakken iko da suka haɗa da hawa kujerar naki
- Hakazalika, ta kuma buƙaci nahiyar Afirka ta samu kujeru biyar a Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya
- Najeriya ta yi kira da a fifita diflomasiyya, dokokin ƙasa da ƙasa, kare fararen hula da samar da tallafin kuɗi mai sauƙi ga ƙasashe masu tasowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin New York, Amurka - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya wakilci mai girma Bola Tinubu a babban taron majalisar dinkin duniya (UNGA), karo na 81.
An gudanar da babban taron na UNGA ne a kasar Amurka, inda shugabannin kasashe da dama suka gabatar da jawabansu.

Source: Facebook
A yayin jawabinsa na ranar Alhamis, 24 ga watan Satumban 2026, Kashim Shettima ya bayyana abubuwan da Najeriya ta ke bukatar a aiwatar.
Ga muhimman abubuwan da Najeriya ta neman a wajen taron:
1. Garambawul a kwamitin tsaro na UN
Najeriya ta sake yin kira da a yi wa Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya garambawul, tana mai cewa Afirka na buƙatar samun wakilcin da ya dace a cikin tsarin yanke shawarar Majalisar, tashar Channels tv ta kawo rahoton.
Najeriya ta buƙaci, bisa yarjejeniyar Ezulwini da Sirte, a bai wa Afirka kujerun dindindin biyu masu cikakken iko, ciki har da ikon amfani da kuri’ar hawa kujerar naki muddin ana ci gaba da amfani da wannan tsarin.
Ta kuma buƙaci Afirka ta samu kujeru biyar wadanda ba na dindindin ba a Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya.
2. Komawa kan ka'idojin da aka kafa UN a kansu
Najeriya ta ce garambawul ɗin ya kamata ya mayar da majalisar dinkin duniya kan ƙa’idojin da aka kafa ta a kansu, musamman tattaunawa, mutunta juna da ɗaukar nauyin al’amuran duniya tare.

Kara karanta wannan
Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya
Ta jaddada cewa ya kamata diflomasiyya ta rinjayi tilastawa, yayin da dokokin ƙasa da ƙasa suka rinjayi amfani da ƙarfin iko ba tare da ƙa’ida ba.
3. Amfani da diflomasiyya don magance rikice-rikice
Najeriya ta yi kira da a gaggauta amfani da diflomasiyya wajen magance rikice-rikice a duniya, musamman yaƙin da ake fama da shi a Sudan da sauran ƙasashen da ke fama da rikici.
Ta kuma buƙaci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa na jinƙai da kuma dokokin kare haƙƙin ɗan Adam, jaridar The Cable ta kawo rahoton.
4. Kare fararen hula
Najeriya ta ce dole ne a kare fararen hula tare da tabbatar da cewa agajin jinƙai ya isa ga mutanen da rikice-rikice suka shafa.
Hakazalika, ta kuma bukaci a rika samar da kayan agaji ga fararen hular da rikice-rikice suka ritsa da su.
5. Sauya tsarin kuɗi na duniya
Najeriya ta kuma yi kira da a yi garambawul ga tsarin kuɗi na duniya, tare da faɗaɗa damar ƙasashe masu tasowa samun rancen kuɗi masu sauƙin sharadi.
Ta ce ya kamata tsarin kula da ɗorewar bashi ya yi la’akari da buƙatun ƙasashe masu tasowa da halin da tattalin arzikinsu yake ciki.

Kara karanta wannan
"Za a iya cikin kwanaki 7"; Iran ta sanar da Amurka sharadin bude mashigar Hormuz
6. Kara karfafa ayyukan kwantar da tarzoma
Najeriya ta yi kira ga majalisar dinkin duniya ta kara karfafa ayyukan kwantar da tarzoma a wuraren da ake rikice-rikice.
Hakazalika, ta kuma bukaci a mayar da hankali sosai wajen sasanta rikici da kuma samar da cibiyoyin da za su kawo ci gaba a kasashe.
7. Najeriya ta nemi ƙarin haɗin gwiwa kan tsaro
Najeriya ta kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe wajen yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro da ke ƙetare iyakokin ƙasa.
Ta buƙaci ƙasashe su riƙa musayar bayanan sirri, dakile hanyoyin da ake bi wajen samar da kuɗin tallafa wa ayyukan ta'addanci da kuma hana haramtattun makamai ketare iyakokin ƙasashe.
Shettima ya ce doguwar fafutukar da Najeriya ta yi da Boko Haram, ISWAP da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ta koya mata cewa nasarar soja kaɗai ta yi kadan wajen kawo zaman lafiya mai ɗorewa.

Source: Facebook
An yi wa Netanyahu ihu a UNGA
A wani labarin kuma, kun ji cewa wakilai daga ƙasashe da dama sun fice daga zauren Majalisar Ɗinkin Duniya yayin da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fara gabatar da jawabinsa.
Wasu daga cikin wakilan sun yi ihu da fito yayin da Netanyahu ke fara jawabi, yayin da ’yan tawagarsa suka tsaya suna tafa masa.
Asali: Legit.ng

