Babbar Magana: Abin da Zai Faru da Masu Zagi da Sukar Gwamnatin Tinubu
- Mai girma Bola Tinubu ya yi magana kan suka da hantarar da wasu ke yi wa gwamnatinsa a Najeriya
- Shugaban kasar ya ce jure suka na daga cikin ginshiƙan ajandar Renewed Hope da kuma ƙudurin gwamnatinsa na kare ’yancin kafafen yaɗa labarai
- Tinubu ya bayyana sauye-sauyen gwamnatinsa a matsayin matakan da za su sauya alkiblar Najeriya tare da ƙarfafa tattalin arziki da cibiyoyin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda gwamnatinsa ta kasance tana jure suka da kalamai masu zafi ba tare da ɗaukar matakin ramuwar gayya ba.
Shugaba Tinubu ya ce ’yan Najeriya na iya zaginsa ko sukarsa, amma su koma gidajensu su kwanta lafiya ba tare da fargabar wata matsala da daddare ba.

Source: Getty Images
Jaridar Vanguard ta ce Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026 yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar kamfanin Daily Times of Nigeria Limited, wanda aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
"Na samu labari mara dadi"; Atiku ya haska matsalar da matasa ke fuskanta a gwamnatin Tinubu
Shugaban ƙasa bai halarci taron da kansa ba, sai dai Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya wakilce shi.
Tinubu ya ce akwai 'yancin kafafen yaɗa labarai
A cewar Tinubu, jure suka na daga cikin muhimman ginshiƙan ajandar gwamnatinsa ta Renewed Hope Agenda da kuma ƙudirin kare ’yancin kafafen yaɗa labarai.
Akume ya karanta saƙon shugaban, inda Tinubu ya ce:
“Mu amince cewa a ƙarƙashin wannan gwamnati, za ka iya zagi ko ka soki shugaban ƙasa, amma har yanzu ka koma ka kwanta ba tare da wata matsala da tsakar dare ba. Wannan falsafa ce a ajandar Renewed Hope.”
Tinubu ya ce ya fahimci muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tsara makomar ƙasa da kuma wayar da kan al’umma.
Kalubalen Najeriya sun samo asali tun da daɗewa
Shugaba Tinubu ya ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu ba su samo asali cikin dare ɗaya ba.
A cewarsa, wasu daga cikin ƙalubalen ƙasar sun samo tushe ne daga raunin tsarin mulki da tattalin arziki da suka taru tsawon shekaru da dama.
Ya ce aikin farfaɗo da ƙasa na buƙatar jajircewa wajen fahimtar inda Najeriya ta fito, da kuma fuskantar abubuwan da aka bari suka zama masu wahalar magancewa.
Tinubu ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta yanke wasu muhimman matakai domin tabbatar da cewa ƙasar ta samu damar kai wa inda ya kamata ta kasance.
Tinubu ya kare manufofin gwamnatinsa
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fi sauya manufofin gwamnati kawai.
Ya ce manufar sauye-sauyen ita ce sauya alkiblar Najeriya, tare da samar da ingantaccen tsarin kuɗaɗen gwamnati da gina tattalin arziki mai samar da abubuwa.
Hakazalika, ya ce gwamnatin na kuma ƙoƙarin ƙarfafa hukumomi, jawo masu zuba jari, inganta ababen more rayuwa da faɗaɗa damar da matasa za su samu.
A cewarsa, waɗannan matakai za su taimaka wa Najeriya ta yi gogayya da sauran ƙasashe a tattalin arzikin duniya cikin ma’ana da manufa.

Source: Twitter
'Yan kabilar Igbo sun marawa Tinubu baya
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan kabilar Igbo mazauna jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun yanke shawarar marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.
'Yan kabilar ta Igbo sun kuma bayyana aniyarsu ta tallafa wa jam’iyyar APC tare da ƙudirin samar wa shugaban ƙasa aƙalla ƙuri’u miliyan biyu.
Asali: Legit.ng

