Sarki Sanusi II Ya Haska a Majalisar Dinkin Duniya, Ya Wakilci Abba Kabir

Sarki Sanusi II Ya Haska a Majalisar Dinkin Duniya, Ya Wakilci Abba Kabir

  • Mai Martaba Sarki, Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi, ya wakilci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a wani taro da aka gudanar yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York
  • Sarki Sanusi ya halarci tarurruka da dama da suka mayar da hankali kan makamashi, noma, ma’adinai da bunƙasa tattalin arzikin Afirka
  • Haka kuma, Sarkin Kano ya gana da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a masaukinsa da ke New York, inda suka tattauna kan batutuwan ƙasa, al’umma da ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

New York, Amurka – Mai Martaba Sarki, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya wakilci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a wani taron gefe da aka gudanar a yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a birnin New York.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya yi magana kan kara albashin ma'aikatan Najeriya

Mai Martaba ya halarci taron, inda ya shiga tattaunawa kan samar da wutar lantarki domin bunƙasa noma, ma’adinai, masana’antu da fasahar zamani.

Sarki Muhammadu Sanusi II
Sarki Sanusi II a wajen taron UN. Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai game da abubuwan da Sarki Sanusi II ya yi ne a wani sako da fadar sarkin Kano ta wallafa a shafinta na X.

Sanusi ya halarci taron makamashi

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannonin makamashi da tattalin arziki, inda aka tattauna kan yadda ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki zai taimaka wajen haɓaka ayyukan noma, ma’adinai da fasahar zamani.

Rahoto ya nuna cewa the Global African ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar AP3, DalaHill, TAO da SurFi.

Sarki Sanusi ya shiga tattaunawar Fireside Chat, inda aka mayar da hankali kan rawar makamashi wajen ƙara yawan aiki da bunƙasa sassa daban-daban na tattalin arzikin Najeriya.

Taron albarkatun ma’adinai

A ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, Sarki Sanusi ya halarci wani taro da ya shafi harkokin ma'adinai a birnin a New York.

Taron ya mayar da hankali kan damar da Afirka ke da ita wajen amfani da albarkatun ma’adinai masu muhimmanci domin ƙarfafa tattalin arziki da samar da ci gaba.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Shettima ya fada kan Najeriya a taron majalisar dinkin duniya

An gudanar da taron ne cikin tarurrukan gefe da ake gudanarwa yayin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 da ke gudana a birnin New York.

Sarki Sanusi ya gana da Shettima

A ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2026, Mai Martaba Sarkin Kano ya gana da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a masaukinsa da ke New York.

Ganawar ta kasance wata dama da shugabannin biyu suka tattauna kan wasu batutuwa da suka shafi Najeriya, al’umma da ci gaba yayin da suke halartar ayyukan da suka shafi taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Jawabin da Shettima ya yi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya sake yin kira da a yi gagarumin garambawul a Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman ta hanyar sake fasalin Majalisar Tsaro.

Shettima ya ce ya kamata Afirka ta samu aƙalla kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da samun cikakken iko.

Ya ce ya kamata a kuma bai wa nahiyar kujeru biyar na wucin gadi, yana mai cewa tsarin rarraba ƙarfin duniya na shekarar 1945 bai kamata ya ci gaba da zama ginshiƙin tsarin duniya na shekarar 2026 ba..

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng