Gwamna Ya Je Birtaniya Ya Gano Farashin Fetur, Ya Fadi Abin da Ya Gani
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya ce litar fetur a Birtaniya tana kaiwa sama da N3,000 idan aka sauya farashin zuwa Naira
- Okpebholo ya ce Najeriya na samun sauƙi idan aka kwatanta farashin fetur da na Birtaniya, inda ya yaba da matakan Shugaba Bola Tinubu
- Ya bayyana Tinubu a matsayin masanin tattalin arziƙi da ke ɗaukar matakan da suka dace domin daidaita tattalin arziƙin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ce farashin litar fetur a Birtaniya ya haura N3,000.
Gwamnan na Edo ya bayyana cewa Najeriya na samun sauki a farashin da ake sayar da man fetur a yanzu.

Source: Facebook
Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta ta X ranar Juma’a, 25 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya gano abin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wahala bayan cire tallafin fetur
Gwamnan ya kuma ce Najeriya tana cikin “amintattun hannaye” karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Okpebholo ya je Birtaniya ya duba farashin fetur
Gwamna Monday Okpebholo ya ce yayin da ake korafi kan tsadar fetur a Najeriya, ya kasance a birnin Landan a makon da ya gabata.
Ya ce ya je sayen fetur tare da wasu abokansa domin su kwatanta farashin man fetur tsakanin Najeriya da Birtaniya.
“Na gaya wa abokaina, mu je mu sayi fetur kawai domin mu san farashin fetur tsakanin Najeriya da Ingila."
“Bari na gaya muku. Bayan an sauya kudin, ya kai kusan N3,000 da wani abu kan litar fetur. Muna yin abin kirki a nan.” In ji shi.
Farashin fetur a Najeriya da Birtaniya
Ya zuwa ranar 24 ga Satumba, matsakaicin farashin litar fetur a Birtaniya ya kai kusan fam £1.74, wanda ya yi daidai da sama da N3,000 idan aka yi amfani da farashin canjin kudin da ake samu a lokacin.
A Najeriya kuwa, sabon jadawalin farashin famfunan man fetur na Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC Limited) ya nuna cewa ana sayar da litar fetur kan N1,385 a Legas da N1,430 a Abuja.
Sai dai farashin da ake sayar da man fetur yana bambanta daga wuri zuwa wuri a fadin ƙasar.
Okpebholo ya yaba wa Tinubu
Okpebholo ya kuma bayyana Shugaba Tinubu a matsayin masanin tattalin arziƙi da ke ɗaukar matakan da ya dace domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar.
“Shugabanmu ba ɗan kasuwar babban shago ba ne. Mutanen babban shago, su jira. Idan lokacin da ɗan kasuwa ya mallaki shugabancin Najeriya ya zo, kuma masana tattalin arziƙi ba su nan, to sai su zo.” In ji shi.
Gwamna Monday Okpebholo ya ce Najeriya tana cikin “amintattun hannaye” karkashin gwamnatin Tinubu.

Source: Facebook
Dangote da 'yan kasuwa sun sauke farashin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote da sauran dillalan man fetur sun rage farashin man fetur a wasu manyan ma’ajiyoyi a Najeriya.
Lagos, matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N1,350 zuwa N1,325, wanda ke nufin an rage N25 kan kowace lita.
Asali: Legit.ng
