Christopher Musa Ya Yi wa Kwankwaso da Obi Raddi, Ya Ce Tinubu zai Zarce

Christopher Musa Ya Yi wa Kwankwaso da Obi Raddi, Ya Ce Tinubu zai Zarce

  • Ministan Tsaro, Christopher Musa ya yi watsi da ikirarin 'yan takarar jam'iyyar NDC, Peter Obi da Dr Rabiu Kwankwaso, na cewa za a iya kayar da shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Musa ya nuna kyakkyawan kwarin gwiwar cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta sake lashe zaben shugaban ƙasa, na gwamna, da sauran mukamai a jihar Kaduna da kuma ƙasa baki ɗaya
  • Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis da manema labarai, inda ya buƙaci 'yan Najeriya da su kara hakuri da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya fito fili ya bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta samu nasara a zaben shugaban ƙasa da na gwamnan jihar Kaduna a zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

'Za a mutu,' Obi ya yi gargadi mai zafi kan magudi a zaben 2027

Musa ya musa kalaman 'yan takara na jam'iyyar NDC, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, waɗanda suka bayyana cewa jam'iyya mai mulki za ta iya faduwa zaɓe duk da irin jihohin da ke ƙarƙashinta.

Christopher Musa da Bola Tinubu
Christopher Musa a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Janar Musa mai ritaya ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na gidan talabijin na Channels.

Maganar nasarar APC a Kaduna

Da ake tambayarsa game da yiwuwar korar APC daga mulki a jihar Kaduna saboda halin da ake ciki, Musa ya bayyana cewa ra'ayin mutane daban-daban ne kuma jam'iyyarsa ce za ta yi nasara a dukkan matakai.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

"Wannan ra'ayi ne kawai. Ra'ayi ne, kuma kowa yana da ra'ayinsa. Mutane a ko da yaushe suna fadin ra'ayi na daidai ko akasin haka.
"Ba zan ce za a iya faduwa ba; APC za ta yi nasara a Kaduna. A matakin shugaban ƙasa, gwamna, da dukkan matakai."

Ministan ya kuma yi watsi da maganar cewa farin jinin Shugaba Tinubu yana raguwa a shiyyar Arewa, inda ya zargi wasu 'yan siyasa da amfani da yanayin da ake ciki wajen ruruta lamarin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ministan tsaro ya yi zarge zarge kan El Rufa'i da ke tsare

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu da mataimakinsa a zaben 2027, Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu

Ministan ya kare manufofi da gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu take gudanarwa, yana mai jaddada cewa shugaban ya ɗauki tsauraran matakan da suke buƙatar lokaci kafin su fara fitar da sakamako mai kyau.

Ya bukaci 'yan Najeriya da su kasance masu haƙuri da gwamnati mai ci, tare da nuna kwarin gwiwar cewa alfanun tsare-tsaren zai fito fili sannu a hankali.

Shawawar Atiku ga Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya janye daga takarar shekarar 2027.

Atiku ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya nemi gafararsa da ta 'yan Najeriya kan raina shawarar da ya bayar ta tallafawa fannin tace man fetur na cikin gida.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne ta hanyar sanarwa daga mai magana da yawunsa Phrank Shaibu, biyo bayan kiran da IPMAN ta yi kan tsadar mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng