Bashin Biliyoyi Ya Taru a kan Kiyosaki da ke Koya wa Mutane Dabarun Yin Kudi

Bashin Biliyoyi Ya Taru a kan Kiyosaki da ke Koya wa Mutane Dabarun Yin Kudi

  • Marubucin littafin “Rich Dad Poor Dad”, Robert Kiyosaki, ya bayyana cewa ana bin shi bashin dala biliyan 1.2 a yanzu haka
  • Kiyosaki, mai shekaru 79, ya sha bayyana adadin bashin, yana mai cewa yana yin rance domin sayen kadarorin da ke samar da kuɗi
  • Sai dai tsohuwar matarsa kuma abokiyar kasuwancinsa, Kim Kiyosaki, ta ce mutane ba su fahimci batun bashin daidai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Marubucin shahararren littafin koyar da dabarun samun kuɗi, “Rich Dad Poor Dad”, Robert Kiyosaki, ya bayyana cewa ana bin shi bashin dala biliyan 1.2 da ya danganci jarinsa na gidaje da kadarori.

Kiyosaki ya sha bayyana wannan adadi, inda yake cewa rance domin sayen kadarorin da ke samar da kuɗin shiga wata hanya ce da attajirai ke amfani da ita wajen haɓaka dukiyarsu.

Kara karanta wannan

A karshe, an gano wanda ya kashe mawakin duniya Tupac Shakur

Littafin Robert Kiyosaki
Fitaccen littafin da Robert Kiyosaki ya wallafa. Hoto: Rich Dad Poor Dad
Source: Facebook

Ana bin Kiyosaki bashi

New York Post ta wallafa cewa Kiyosaki ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin da ya ke koyar da mutane dabarun samun kudi.

Yayin da ya ke yi wa jama'a bayani, Kiyosaki ya ce:

“Don haka, ana bi na bashin dala biliyan 1.2.”

Ya kuma yi gargaɗin cewa mutane ba lallai ne su yi koyi da salon harkokinsa ba:

“Bai kamata ku yi abin da nake yi ba, ko?”

Yadda bashi ya hau kansa

Tsohuwar matar Kiyosaki kuma abokiyar kasuwancinsa, Kim Kiyosaki, ta bayyana cewa ba a fahimci adadin dala biliyan 1.2 da aka danganta da bashin Kiyosaki ba.

Kim ta shaida cewa ita da Kiyosaki suna da gidajen haya da dama tare da abokan hulɗarsu, waɗanda adadinsu ya kai kusan gidaje 1,500.

Ta ce bashin yana kan kadarorin ne, kuma kaso ɗan ƙarami ne kawai ke cikin abin da Kiyosaki yake da alhakin biya kai tsaye.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Yadda yake amfani da bashin

A cewar Vanity Fair, babbar hanyar da ta haifar da bashin ita ce dabarar Kiyosaki ta amfani da ƙarin darajar kadarorinsa wajen karɓar wasu rance.

Yayin da darajar kadarorin ke ƙaruwa, Kiyosaki na iya karɓar ƙarin kuɗi bisa wannan ƙimar, sannan ya yi amfani da kuɗin a matsayin hanyar samun kuɗi ba tare da sayar da kadarorin ba.

Har ila yau, yana sanya wasu daga cikin jarinsa a cikin kamfanonin LLC daban-daban domin kare su daga matsalolin da ka iya tasowa a wani ɓangare na jarinsa.

Robert Kiyosaki a shekarun baya
Attajiri Robert Kiyosaki a shekarar 2006. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton NDTV ya nuna cewa Kiyosaki ya ce:

“Za ku iya magana da lauyana.”

Ya sayar da littafi sosai

Kiyosaki ya gina babbar cibiyar koyar da harkokin kuɗi ne ta hanyar littafinsa na “Rich Dad Poor Dad”, wanda aka fara wallafa shi a shekarar 1997, inda ya sayar da kwafi sama da miliyan 44 a duniya.

Littafin ya kwatanta darussan da Kiyosaki ya ce ya koya daga mahaifinsa, wanda ya kira “Poor Dad”, da kuma waɗanda ya ce ya koya daga mahaifin babban abokinsa na ƙuruciya, wanda ya kira “Rich Dad”.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Mahaifinsa, Ralph Kiyosaki, ya taɓa zama babban jami’in kula da ilimi na jihar Hawaii, sannan ya tsaya takarar mataimakin gwamnan jihar a shekarar 1970 amma bai yi nasara ba.

Daga baya Kiyosaki ya bayyana “Rich Dad” ɗinsa a matsayin Richard Kimi, wani ɗan kasuwa a Hawaii wanda ya mallaki jerin otal-otal da suka haɗa da Waikiki Biltmore.

Batun kashe Tupac Shakur

A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu tsohon shugaban wata ƙungiyar masu laifi, Duane “Keffe D” Davis, da laifin shirya kisan fitaccen mawaki Tupac Shakur.

Kotun Las Vegas ta same shi da laifin kisa da makami, dangane da harin da aka kai wa Tupac a wani harbin mota a ranar 7 ga Satumba, 1996.

A lokacin shari’ar, an saurari wani faifan hirar da ‘yan sanda suka yi da Davis a shekarar 2008, inda ya ce yana cikin motar da aka yi harbin daga cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng