Yadda aka Jefar da Jarirai a Kango cikin ban Tausayi bayan an Haife Su a Abuja

Yadda aka Jefar da Jarirai a Kango cikin ban Tausayi bayan an Haife Su a Abuja

  • Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta ceto wasu jarirai biyu da aka jefar da su a wasu wurare daban-daban a Kurudu da Gwagwalada
  • An gano jariri a cikin kwali a Kurudu, yayin da aka gano jaririya a wajen wani gida a Gwagwalada bayan mazauna yankin sun ji kukanta
  • Rundunar ta nemi jama’a da ke da bayanan da za su taimaka wajen gano iyayen ko ’yan uwan jariran da su sanar da ’yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta ceto jarirai biyu da aka jefar da su a wasu wurare daban-daban a Kurudu da Gwagwalada.

Rundunar ta ce lamarin na farko ya faru ne ranar Laraba, 2 ga Satumba, 2026, da misalin karfe 5:45 na yamma, bayan wani mazaunin Kurudu mai suna Innocent ya kai rahoto ofishin ’yan sanda.

Kara karanta wannan

An kama Kirista ta yi shigar Musulunci tana satar yara a Abuja

Jariran da aka jefar a Abuja
Kakakin 'yan sanda dauke da jariran da aka samu. Hoto: FCT Command Abuja
Source: Facebook

Bayanin da 'yan sanda suka wallafa a Facebook ya ce Innocent da misalin karfe 5:30 na yamma ya ji kukan jariri, inda bayan ya duba sai ya gano jaririn a nade cikin zani kuma an bar shi a cikin kwali.

An ceto jariri a Kurudu

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda daga sashen Kurudu tare da jami’an sashen kula da yara da mata (JWC) suka je wurin.

Jami’an sun gano jariri namiji tare da ceto shi, sannan aka kai shi wani asibiti da ke kusa domin duba lafiyarsa.

Rundunar ta ce jaririn na cikin koshin lafiya, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa aka yi watsi da shi.

Bayan kammala dukkan takardun da suka dace, rundunar ta mika jaririn ga sashen jin dadin jama’a domin ci gaba da kula da shi.

Taswirar FCT Abuja
Taswirar FCT Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An samu jaririya a Gwagwalada

A wani lamari makamancin haka, a wannan rana da misalin karfe 9:40 na dare, wani mazaunin Gwagwalada mai suna Ibrahim ya ji kukan jariri a wajen kofar gidansa.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke likitoci, lauyoyi da masu ba 'yan bindiga bayanai

Bayan ya duba, sai ya gano jaririyar da ake ganin an yi watsi da ita a harabar gidan.

Ibrahim tare da wasu mazauna yankin masu kishin al’umma sun ceto jaririyar tare da kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Gwagwalada da misalin karfe 10:15 na dare.

An kai jaririyar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja domin duba lafiyarta, inda a yanzu take samun kulawa kafin mika ta ga sashen jin dadin jama’a.

An kama mata 2 a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan FCT ta sake kama wasu mata, Rose Daniel da Blessing John, bisa zargin satar yara sanye da hijabi.

An kama matan biyu ne ranar 27 ga Agustan 2026 yayin da ake zargin suna kokarin tserewa da yarinyar mai suna Ummi Mariam Abdullah.

Binciken farko ya nuna cewa an taba kama wadanda ake zargin a watan Disambar 2025 kan irin wannan laifi, inda daga bisani aka same su da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng