Atiku Ya Ziyarci Neja, Ya ba da Tallafi ga Iyalan Mutanen da Suka Mutu a Hannun NSCDC
- Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya ziyarci Minna, inda ya jajanta wa Sarkin Minna da iyalan masu haƙar ma’adanai 37
- Atiku ya bayar da tallafin N20m ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu a lamarin da ya faru a hannun NSCDC
- Ya ce gwamnati na bukatar sake duba manufofin tattalin arziki domin rage tsadar rayuwa da samar da damar aiki ga matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci Minna, babban birnin Jihar Neja, domin jajanta wa al’ummar jihar kan wasu munanan abubuwan da suka faru.
Atiku ya fara ziyartar Mai Martaba Sarkin Minna kuma Shugaban Majalisar Masarautar Minna, Alhaji (Dr.) Umar Farouk Bahago, inda ya mika sakon ta’aziyyarsa.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa kan Sadarwar Jama’a, Phrank Shaibu ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Atiku ya ba da tallafin N20m
A yayin ganawarsa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa, Atiku ya sanar da bayar da tallafin N20m domin taimaka wa mutanen da suka rasa ’yan uwansu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce Najeriya ba za ta iya tabbatar da makomarta ba tare da zuba jari ga matasa, faɗaɗa damar da suke da ita da kuma ba su damar gudanar da sana’o’in halal da za su amfani al’umma ba
Atiku ya bayyana mutuwar matasan a matsayin abin takaici da ke nuna irin halin ƙuncin da matasan Najeriya ke fuskanta.
Atiku ya yi takaicin abin da ya faru
Atiku ya ce ya ji takaici sosai bayan ya saurari bayanin wani daga cikin waɗanda suka tsira daga lamarin, jaridar The Punch ta dauko labarin.
Ya ce mutumin ya bayyana cewa an cunkusa sama da mutane 68 a wani ƙaramin wuri, inda yanayin ya tsananta har suka tilasta wa juna shan fitsari domin samun ruwa.

Kara karanta wannan
Tinubu na tsaka mai wuya, sama da 67% na yan Najeriya na so a dawo da tallafin fetur
Atiku ya ce bai kamata wani ɗan Najeriya ya fuskanci irin wannan wulaƙanci a hannun gwamnati ba.
Ya ce mutanen da ake tsare da su mutane ne da gwamnati ke da alhakin kula da su, kuma ko da kuwa ana zarginsu da laifi, suna da haƙƙin rayuwa, mutunci da kariyar doka.
Ya danganta lamarin da matsin tattalin arziki
Atiku ya ce yadda matasa da dama ke shiga sana’o’in da ke da haɗari kuma ba su da cikakken tsari ya kamata ya sa gwamnati ta fuskanci matsalolin talauci, rashin aikin yi da tsadar rayuwa.
Ya ce mutane 37 sun shiga hannun gwamnati suna raye amma ba su koma ga iyalansu da rai ba, yana mai cewa wannan lamari na buƙatar gaskiya, adalci da ɗaukar alhaki.
Ya kuma ce baya ga binciken abin da ya faru a wurin da ake tsare da su, ya kamata a tambayi dalilin da ya sa matasa ke shiga sana’o’in da ke jefa rayukansu cikin haɗari domin kawai su samu abin dogaro da kai.
Atiku ya soki tasirin manufofin Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce mutuwar matasan ya kamata ta sa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi nazari kan illar manufofin tattalin arziki ga rayuwar talakawa.
Ya ce idan iyalai sun kasa samun abubuwan yau da kullum, sannan matasa suka fara ɗaukar manyan haɗurra domin neman abin masarufi, gwamnati ba za ta yi kamar komai yana tafiya daidai ba.
Atiku ya ce ya kamata a auna sauye-sauyen tattalin arziki da irin tasirinsu ga rayuwar talakawa, ma’aikata da matasa.
Ya sake alkawarin rage tsadar rayuwa
Atiku ya sake bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, zai aiwatar da manufofin rage tsadar rayuwa.
Ya ce daga cikin matakan akwai tallafin da za a bai wa man fetur da aka tace a cikin Najeriya, maimakon komawa tsarin tallafin man fetur da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.

Source: Original
MURIC ta yi magana kan kama Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta yi gargaɗi ga gwamnatin tarayya kan kama Atiku Abubakar, bisa zarge-zargen rashin gaskiya a harkokin kudi.
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi taka-tsantsan wajen tafiyar da lamarin da ya shafi Atiku, musamman saboda kusancin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


